Shugabar mata ta Jam’iyyar ADC ta jihar Kano ta yi kira ga mata su fito don yin rajistar katin  zaɓe

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An yi kira ga al’ummar jihar Kano musamman iyaye mata  su fito domin yin rijista da karɓar  katin zaɓe da hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta ta dawo take gudanarwa a halin yanzu a faɗin ƙasar nan.

Shugabar Mata ta Jam’iyyar ADC ta jihar Kano Sayyida Hajiya Maryam Sani Rogo ce ta yi kiran da take zantawa da manema labarai ta ce katin zaɓen yana da mutuƙar muhimmanci wajen zaɓen ra’ayinsu.

Ta ƙara da jaddada cewa katin zaɓen shine tamkar muhimmin makami da za a yi amfani da shi wajen tabbatar da an zaɓi shugabanni nagari masu nagarta da za su kyautata cigaban al’umma.

Ta yi nuni da cewa a harkar yin zaɓe mata da matasa sune ƙashin baya da suka fi tsayawa kyam  da jajircewa kuma mallakar katin zaɓe shi ne zai bayar da dama mata su kare yancinsu na zaɓe a tsarin dimukuraɗiyya su zaɓi wanda zai taimaki cigaban al’umma. 

Hajiya Sayyida Maryam Sani Rogo ta yi kira ga al’ummar jihar Kano da na ƙasar nan baki ɗaya akan su rungumi tafiyar jam’iyyar su ta ADC domin ita ce za ta kawo sauyi da kawo ɗauki domin ceto al’umma daga ƙuncin rayuwa, barazanar tsaro da ɗimbin matsaloli da suka dabaibaye ƙasar nan.

By ukarofi