Sin: Matakin da Amurka ta ɗauka babakere ne ta fannin kimiyya

Daga CMG HAUSA

A game da yadda ƙasar Amurka ta tsaurara matakan ƙayyade fitar da kayayyaki zuwa ƙasar Sin, ta ɓangarorin haɗa na’urorin latironi na “semi conductor”, kakakin ma’aikatar kasuwanci ta ƙasar Sin ta bayyana cewa, wannan babakere ne na zahiri ta fannin kimiyya.

A cewar kakakin, hakan ya saba wa manufar haɗin gwiwar ƙasashen biyu, har ma ya haifar da tsaiko ga mu’amalar dake tsakanin kamfanonin ƙasashen biyu, baya ga kuma yadda hakan ya keta dokokin kasuwanci da ma tsarin tattalin arziki da ciniki na duniya, tare da haifar da barazana ga tsarin samar da kayayyaki na duniya, don haka, ƙasar Sin ta bayyana rashin amincewarta da kakkausar murya.

Kakakin ta ƙara da cewa, kamata ya yi Amurka ta dakatar da wannan mataki na kuskure nan da nan, kuma ta yi wa kamfanonin ƙasar Sin da na sauran ƙasashe adalci.

Ƙasar Sin ta kuma yi kira ga sassan ƙasa da ƙasa, da su inganta haɗin gwiwa, don kafa tsarin samar da kayayyaki mai inganci, wanda zai amfani ƙasa da ƙasa.

Mai fassara: Lubabatu Lei