Asusun CFRD ya samu yabo a ƙasar Habasha

Daga CMG HAUSA

Asusun raya karkara na ƙasar Sin ko CFRD a taƙaice, ya samu yabo da jinjina, bisa managartar ayyukansa a ƙasar Habasha, a gabar da aka yi bikin cikarsa shekaru 3 da buɗe ofishinsa a ƙasar Habasha.

Asusun CFRD ya fara gudanar da ayyuka daban daban a Habasha tun daga shekarar 2015, an kuma yi masa rajistar gudanar da ayyuka a matsayin asusun ba da tallafin jin kai na ƙasa da ƙasa a ƙasar a watan Yulin shekarar 2019, inda ya maida hankali ga zurfafa haɗin gwiwar musaya tsakanin al’ummun Sin da na ƙasar Habasha.

Da yake jawabi yayin bikin na jiya Litinin, babban daraktan ƙungiyoyin masu zaman kansu na ƙasar Habasha Jima Dilbo, ya ce asusun CFRD ya shafe shekaru 7 yana gudanar da ayyuka daban daban a Habasha, ciki har da ciyar da daliban makarantu, da raba kayan karatu, da kayan abinci, da ruwan sha da ayyukan tsaftar muhalli, da ayyukan bunƙasa tattalin arzikin mata, ayyukan da suka amfani sama da ’yan ƙasar Habashan 250,000.

Mr. Dilbo ya ƙara da cewa, dukkanin ayyukan CFRD, sun yi daidai da muhimman ayyukan da gwamnati da al’ummun Habasha ke buƙata, waɗanda ke da matukar tasiri ga ci gaban ƙasar.

Jami’in ya kuma yi kira ga asusun na CFRD, da ya jagoranci ƙungiyoyi masu zaman kansu dake Habasha, wajen ƙulla alaƙa da sauran ƙungiyoyin da hukumomi na ƙasa da ƙasa, kamar shirin samar da ci gaba na ƙasa da ƙasa, da na haɗin gwiwar bunƙasa ƙasashe masu tasowa, da shirin ziri ɗaya da hanya ɗaya.

Mai fassara: Saminu Alhassan