Abinda ya sa na shirya fim kan matsalar ƙwacen waya – Aminu Bala

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU

A yanzu dai masana’antar finafinai ta Kannywood kullum sai ƙara samun ɗaukaka ta ke yi ta fannin cigaban zamani ba kamar a baya ba da a ke kallon ta a matsayin masu harkar fim na waƙoƙi da raye-raye. Dangane da haka ne aka samu wani tsohon jarumi kuma furodusa, Aminu Bala Mailalle, ya shirya wani fim mai dogon zango a kan matsalar qwacen waya. A kan haka ne mu ka tattauna da shi domin jin manufarsa ta shirya wannan fim ɗin mai suna ‘Sawun Giwa’. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.

BLUEPRINT MANHAJA: A kwanakinnan ka saki fim ɗin ka a YouTube mai suna ‘Sawun Giwa’, ko za ka faɗa mana manufarka ta shirya wannan fim ɗin?

AMINU MAILALLE: To shi wannan fim pSawun Giwa’ na shirya shi ne a kan matsalar ƙwacen waya wanda a yanzu abin ya zame mana wata babbar barazana a tsakanin matasanmu, kuma sannan ita harkar waya a yanzu duk wani kasuwancin da a ke yi a yanzu ya ta’alaƙa ga wayar don haka kuma a cikin harkar kasuwancin da a ke yi a waya sai ya zama akwai harƙalla da rashin gaskiya sosai a cikin sa, sai ya zama Irin waɗannan abubuwan su mu ka fi mayar da hankali a wajen faɗakar da jama’a a kan su.

Kuma daga yadda fim ɗin ya fara fita a farkon wannan wata, mun ga yadda mutane suka karɓe shi, kuma da yardar Allah zai shiga cikin finafinai da zai burge jama’a a wannan lokacin, domin zai wa’azantar da kuma nuna wa mutane hanyar da za su bi, don samun kariya a gare su da kuma duniyarsu da suke ajiyewa a banki.

Saboda a yanzu ne za ka yar da wayar ka, kuma da an jima sai ka ji an fara cire ma ka kuɗi a banki, to wannan saƙon da yake cikin fim ɗin zai nuna ma ka yadda kai da kan ka za ka koyi yadda za ka kare kan ka.

Wannan sabon salo ne a cikin harkar fim ta Kannywood. Ko me ya ba ka ƙarfin gwiwar shirya wannan fim ɗin?

To wannan salo, da farko bayan na ɗan ja baya da harkar fim, na shiga kasuwar waya, na fara cinikayya, na buɗe shagona. To na ga harƙalla da rigingimu da fitintinu da waya ta ke haifar wa, don za ka tarar da waya ɗaya ta yi sanadin shigar mutane sama da 20 cikin haɗari, wata ma tsintar ta za ka yi ta kai ka ga shiga yanayi mai wahala. Wata kuma haka kawai za ka je ka sayi waya da kuɗin ka ƙarshe ka je ka tarar ta sata ce.

To a matsayina na ɗan fim na lura mutane da yawa sun kasa gano yadda za su yi mu’amala da ita ta yadda za su kare kan su da kuma duniyarsu. To haka ne ya sa muka zauna mu ka shirya labarin da zai nuna wa mutane hanyar da za su bi su kare kan su cikin sauƙi.

To a yanzu tun da an fara ganin fim ɗin kai a kan ka ya kake ganin yadda jama’a suka karɓi fim ɗin ?

To lallai a yanzu mun fara ganin nasara kuma mu na sa ran nan gaba abin ya wuce haka tun da mu na son mu ci gaba ne ba wai mu tsaya iya nan ba. Kuma Ina son matasa da kuma iyayenmu na gida idan sun kalli fim ɗin su fahimci yadda saƙon yake ta yadda za su san irin mu’amalar da za su yi da wayoyinsu da yadda za ka yi ka fita idan ka samu matsala a game da sarar waya ta wannan lokacin, don haka fim ɗin daman manufarsa faɗakar wa da kuma wayar da kan jama’a da yadda za su yi mu’amalarsu da wayoyinsu.

Ko menene saƙonka na ƙarshe?

To abin da na ke so na faɗa shi ne, Ina kira ga jama’a da kuma sauran kamfanoni da masu hannu da shuni da kuma masu harkar sayar da waya, in da akwai wani abu da suka gani da suka ga mun fara haskawa wanda hankalinmu bai kai ba, mu na neman gudunmawarsu a kowanne lokaci ƙofarmu a buɗe ta ke.

To madalla mun gode. 

Ni ma nagode sosai.

By Editor