Sojoji sun kashe Ali Dogo da mayaƙansa a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar Sojojin Saman Nijeriya (NAF) ta samu nasarar kashe ƙasurgumin ɗan ta’addan nan da ya addabi Jihar Kaduna, Ali Dogo, tare da wasu mutanensa 30.

Rahotanni sun nuna cewa, sojojin dakarun ‘Operation WHIRL Punch’ ne suka fattaki Dogo, wanda aka fi sani da Yellow da mayaƙansa a ƙarshen makon da ya gabata.

Sojojin sun yi wa Yellow da mayaƙan nasa dirar mikiya ne a daidai lokacin da suke tsaka da tattaunawa a gidan Alhaji Gwarzo, inda jirgin yaƙin ya sakar wa ginin wuta ya hallaka su baki ɗaya.

Hakazalika, sojojin sun sake kai samame kan ’yan bindiga a yankin Mando da ke Arewa maso Yammacin Kaduna.

Bayanai sun ce sojoji sun kai samamen ne bayan tattara bayanan sirrin da suka samu game da shirin ’yan bindigar da kuma inda suke.

Mai magana da yawun rundunar sojojin sama, AC Edward Gabkwet, ya tabbatar da nasarorin da suka samu.

Haka nan, ya ce, ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen cigaba da fatattakar ’yan ta’adda da harkokinsu a shiyyar Arewa maso Yamma.