Sin ta fara aikin gina wuri mai sanyi don adana rigakafi a Masar

Daga CMG HAUSA

Kamafin Sinovac na ƙasar Sin ya fara aikin gina wuri mai sanyi don adana alluran riga-kafi a wannan mako, ofishin jakadancin ƙasar Sin a Masar ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Liao Liqiang, jakadan ƙasar Sin a ƙasar Masar, ya bayyana a wajen bikin ƙaddamar da fara aikin a ranar Alhamis cewa, ta hanyar tallafin kamfanin hada magungunan na ƙasar Sin, manyan dakuna masu sanyin za su taimaka wa ƙasar Masar wajen inganta aikin adana riga-kafin.

A cewar jakadan, wurin ajiyar mai faɗin murabbi’in mita 2,800, yana da girman da zai iya ɗaukar alluran riga-kafi miliyan 150 idan aikin ya kammala, kuma zai taimakawa ƙasar Masar wajen cimma burinta na yiwa kashi 70 bisa 100 na al’ummar ƙasar alluran riga-kafin COVID-19 nan da tsakiyar shekarar 2022.

Liao yace, wannan wata gagarumar nasara ce da aka cimma ƙarƙashin haɗin gwiwar Sin da Masar a yaƙi da annobar COVID-19, kuma ƙasar Sin zata cigaba da karfafa haɗin gwiwarta da Masar a fannin kiwon lafiya, sannan zata ƙara bada gudunmawa wajen kyautata zaman rayuywar al’ummar kasar Masar.

A lokacin bikin, Khaled Abdel Ghaffar, ministan ilmi mai zurfi da binciken kimiyya na ƙasar Masar, ya bayyana farin cikinsa tare da gode wa gwamnatin ƙasar Sin, da al’ummar Sinawa, bisa goyon baya da taimakon da suke bayarwa a dogon lokaci don cigaban fannin kiwon lafiyar Masar.

Ghaffar ya ce, sabbin wuraren ajiyar masu sanyi, zasu karawa Masar kaimi wajen aikin samar da riga-kafin a cikin gida, da adanawa, da kuma rarraba riga-kafin, kana zai taimakawa ƙasar Masar don zama wata cibiyar samar da riga-kafi a Afrika da ma yankin gabas ta tsakiya.

Fassarawa: Ahmad