Sin za ta ɗauki managartan matakai don cigaba da tallafa wa ajandar cigaba mai ɗorewa ta MƊD nan da 2030

Spread the love

Daga CMG HAUSA

A yammacin yau ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya jagoranci wani babban taron tattaunawa kan ci gaban duniya ta kafar bidiyo, tare da gabatar da muhimmin jawabi.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, sai al’ummomin ƙasashen duniya suna rayuwa mai kyau ne kadai za a iya samun ɗorewar wadata, da tabbatar da tsaro, da kare haƙƙin dan-Adam.

Ƙasar Sin za ta ɗauki managartan matakai, don ci gaba da tallafawa ajandar samun dauwamammen ci gaba ta MƊD nan da shekarar 2030. Ƙasar Sin za ta kara zuba jari a fannin samar da albarkatu a haɗin gwiwar raya ƙasa da ƙasa, da yin haɗin gwiwa da dukkan ɓangarori, don inganta hadin gwiwa a muhimman fannoni: zurfafa haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa wajen rage fatara da kawar da talauci, da inganta samar da abinci da hanyoyin samar da kayayyaki, da inganta haɗin gwiwar makamashi mai tsafta, ƙarfafa yin bincike da samar da alluran rigakafi cikin haɗin gwiwa, inganta hadin kai a fannin sabbin fasahohi zamani, ya haifar da sabon kuzari ga ci gaban ƙasashe baki daya.

Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa

By Editor