Ya kamata gwamnati ta ɗauki matakin sassauta wa al’umma ƙuncin rayuwa – Ɗanpass

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Ɗaya daga cikin Dattawan Arewa Ɗansaran Kano, Alhaji Gambo Abdullahi Ɗanpass ya yi kira ga mahukuntan ƙasar nan da su ɗauki matakai don sassautawa al’umma, musamman na Arewa halin da suka shiga na ƙuncin rayuwa da suka haɗa da yawan tashin farashin da kayan abinci da na masarufi, wanda ya ce hakan na matuƙar galabaitar da rayuwar al’umma.

Ɗanpass ya yi nuni da cewa yanzu ta kai shinkafa da aka hana shigowa da ita, ta gidan ma da ake nomawa anan na neman ta gagari talaka, sannan noman ma da ake ga damuna ta taho amma a wasu jihohin ma noman ya gagara saboda barazanar rashin tsaro.

Alhaji Gambo Abdullahi Ɗanpass ya ce ya kamata gwamnati ta ɗauki matakai na sassauta halin da talakawa yadda za su samu rahusar rayuwa, yadda za su samu walwala amma muddin aka ce za a cigaba da tafiya a haka a ƙasar nan da ake fama da rashin aikin yi da mai aikin gwamnati ma albashin baya fitowa akan kari abubuwa za su cigaba da damulewa.

Alhaji Gambo Abdullahi Ɗanpass ya ce irin uƙubar rayuwa da ake ciki a ƙasar nan kusan dukkan shugabanni babu adalci a zukatansu; hanyar da za a samu mafita shine kowa ya mallaki katin zaɓe don ranar zaɓe a kauda zalunci don tabbatar da adalci.

Ya nuna mutuqar takaicinsa ga rashin sanin hanyar da gwamnati za ta bi don inganta tattalin arziƙin ƙasa, “kullum sai koma baya ake samu duk da cewa farashin gangar ɗanyen mai ya tashi a kasuwar duniya, amma a ƙasar nan wahala na ƙaruwa, saboda haka jama’a dole a duba a zaɓo shugabanni adilai wanda za su samar da mafita, amma idan aka cigaba da tafiya a haka to ba za a samu mafita ba,” inji shi.

Alhaji Gambo Abdullahi Ɗanpass ya yi kira ga mutane akan a koyawa Allah ayi ta neman gafararsa a zavi shugabanni adilai da suka yi aka gani suka riqe amana.

Haka kuma ya yi kira ga ‘yan kasuwa su dunƙule kansu su shiga siyasa tsundum don su riqa faɗa ana ji wanda zama kara-zube da suke shi ya sa kasuwanci da ƙarfi da yaji yake samun koma baya, ba masana’antu ba kasuwa, dole zaman banza ya ƙaru a riƙa samun barazanar tsaro da ta’addanci.

Ɗanpass ya ce dole ne a samar wa mutane gwamnati tagari wadda za ta kula da haƙƙin jama’a a farfaɗo da masana’antu, sannan kasuwanci ya bunƙasa a cigaba da mu’amala kamar yadda aka saba a baya.