Yadda ɗan banga ya yi wa ‘yar shekara 13 fyaɗe a Nasarawa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Hukumar tsaron farin kaya da aka fi sani da Nigeria Security and Civil Defense Corps a turance na ƙasa reshen Jihar Nasarawa ta cafke wani mataimakin shugaban ‘yan banga mai suna Dalla I. Usman mai kimanin shekaru 42 dangane da aikata laifin fyaɗe wa wata ƙaramar yarinya mai suna Ummi Musa mai kimanin shekaru 13.

Da yake gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai ciki har da wakilin mu a helkwatar hukumar dake Lafiya babban birnin jihar ranar Talata, 22 ga watan Yunin shekarar 2022 da ake ciki, jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, ASC 1 Jerry Victor ya bayyana cewa mummunan lamarin ya afku ne a wani waje dake kusa da Sakatariyar Jam’iyyar PDP a birnin Lafiya fadar gwamnatin jihar bayan ‘yan bangan sun kama yariyar wato Ummi Musa da wasu zannuwa da ta sato daga wani shago, inda suka tsareta a ofishin su don cigaba da gudanar da bincike.

A cewarsa daga nan ne sai wanda ake zargin wato Dalla I. Usman ya yi ta amfani da damarsa na ɗan banga inda ya yi ta lalata da yarinyar a ɓoye har sau uku kafin daga bisani yarinyar ta sanar wa wani yayanta da ya ziyarceta a ofishin ‘yan bangan cewa wanda ake zargin ya yi ta mata fyaɗe a ɓoye.

Daga nan ne sai shi kuma yayan nata ya kai ƙarar ɗan bangan zuwa helkwatar hukumar tsaron inda aka kuma kamo shi.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar ASC 1 Jerry Victor ya cigaba da bayyana cewa, “wannan laifin fyaɗe ne da muke tuhumar wannan mutum wanda ɗan banga ne mai suna Dallah I. Usman ya aikata wa wata ƙaramar yarinya mai suma Ummi Musa mai kimanin shekaru 13 da haihuwa wacce ita ma binciken mu ya gano cewa ‘yan bangan ke zargi da laifin sace wasu zannuwa a wani shago, inda ‘yan bangan suka tsareta a ofishin su dake kusa da babbar sakatariyar Jam’iyyar PDP a birnin Lafiya, fadar gwamnatin jihar nan.

“A yayin da wacce suke zargin wato Ummi Musa ke tsare a ofishin su ɗin ne sai shi wanda ake zargin ya cigaba da yin amfani da damar nasa na ɗan banga inda ya yi ta yi mata fyaɗe har sau uku kafin daga baya jami’an mu suka cafke shi bayan yarinyar ta sanar da wani yayanta lamarin sannan shi kuma ya kawo ƙarar nan ofishinmu.”

Mai magana da yawun ‘yan bangan ya cigaba da cewa: “A halin yanzu dai muna cigaba da gudanar da cikakken bincike akan lamarin. Kuma da zarar mun kammala za mu gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu don ɗaukar matakin da ya dace da aikin ta’asar da ya aikata.

“Kuma har ila yau Ina so in yi amfani da damar nan in yi kira na musamman zuwa ga iyaye da al’umma baki ɗaya cewa su riƙa kula da tarbiyyar ‘ya’yansu su kuma riƙa kai ƙararrakin laifuffuka ko wani da suka kama da laifi ga hukumomin tsaro da suka dace don ƙaurace wa aukuwar ire-iren lamarin nan gaba.”