Siyasar Toro: Yadda za a kaucewa nuna wariyar addini da ƙabilanci

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Kamar yadda kundin sarrafa bayanai na yanar gizo wato Wikipedia ya bayyana Ƙaramar Hukumar Toro da ke Jihar Bauchi a Tarayyar Nijeriya a matsayin ƙaramar hukumar da ta fi kowacce girma a faɗin Nijeriya, ko ma dai a ce yankin Afirka ta Yamma baki ɗaya. Mazaunin Hedkwatar ƙaramar hukumar Toro na yanzu ya tattaro wasu muhimman abubuwa da suka shafi batun da wannan rubutun nawa ya ke son yin nazari a kansu. Amma kafin in fara warware zare da abawar, bari mu ɗan yi waiwaye dangane da matsayin ita kanta Nijeriya, wanda a wani ɗan yanki nata ne ƙasar Toro ta ke. Wannan zai iya zama mana ɗan ba, don a fahimci bayanan da na ke son yin rubutu a kansu, da suka danganci yankin ƙasar Toro da abin da ya bambanta ta da sauran sassan Nijeriya.

Sanannen abu ne kasancewar Nijeriya ƙasa mai yawan ƙabilu. Tana da al’adu da dama da ƙabilu iri-iri, abin da har ake ƙiyasin akwai yaruka fiye da 400 da ƙabilu fiye da 350. Lura da irin waɗannan bambance-bambance, lallai abu ne mai matuƙar wuya tafiyar da su a dunƙule. 

Tun bayan da Nijeriya ta koma tubar dimukraɗiyya a 1999, gwamnatocin baya da aka yi sun yi ta ƙoƙarin ganin sun haɗe kan al’ummar ƙasar a matsayin ƙasa ɗaya al’umma ɗaya. Sai dai cimma nasara wajen tabbatar da wanzuwar taken ƙasar na, haɗin kan mabambantan jama’a, ya zama tamkar mafarki a yanayin da ƙasar ke ciki, da kuma yadda al’ummar ƙasar suke kallon junan su. 

Nuna bambance bambancen addini da ƙabilanci da ya yi yawa a ƙasar ya mayar da ƙasar wajen da shugabanci ya ke da wuyar sha’ani. Yanzu haka a yanayin da mafi akasarin jihohin Nijeriya ke ciki, nazari kan sasanta rikice-rikice ya wuci batun wani Kwas da mutum zai je jami’a ya karanta don a ba shi shaidar kammalawa. Da dama daga cikin Gwamnonin ƙasar nan, yau da gobe ta sa sun zama masana warware saɓani da rikice-rikice a jihohin su, sakamakon irin yadda faɗace-faɗace masu nasaba da addini da ƙabilanci suka yi yawa a jihohin nasu. 

Wannan hali da ake ciki ne ya haifar da yanayin siyasar da yanzu ake gani a ƙasar, siyasar addini da ƙabilanci. Ya zama dole a faɗi gaskiya, wannan mummunan yanayi ya haifar wa qasar koma baya mai yawa. Shi ya sa dole a ja hankalin matasan ’yan siyasa masu tasowa su fahimci irin haɗarin da ke fuskanto su, a matsayin su na manyan gobe, domin samar wa ƙasar makoma tagari. 

Allah ya albarkaci yankin Toro da wasu tsayayyun shugabanni, da suka yi tsayuwar daka, don ganin irin wannan gurɓatacciyar siyasar da nuna bambancin bai samu wurin zama a yankin ba. Shugabanni irin su Alhaji Aliyu Yakubu Lame (Sarkin Yaƙin Bauchi) Hakimi Ƙasar Lame, Alhaji Umar Adamu Toro (Katukan Bauchi ) Hakimi Ƙasar Toro da Alhaji Bala Suleiman Adamu (Ɗan Galadiman Bauchi) Hakimin Ƙasar Jama’a sun daɗe da sadaukar da lokacin su a kan haka.

Waɗannan jajirtattun iyayen ƙasar sun ba da muhimmiyar gudunmawa tare da haɗin gwiwar Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulƙadir Mohammed CON (Ƙauran Bauchi) wajen samun dunƙulalliyar majalisar ƙasar Toro. Tun hawan sa kan kujerar Gwamnan Jihar Bauchi a watan Mayu na shekarar 2019, Gwamnan ya yi ƙoƙarin ganin jihar, musamman ma dai ƙaramar hukumar Toro, da ta ke da iyakoki da jihohin Filato da Kaduna, ta ci gaba da zama cikin zaman lafiya. Ba tare da samun barazanar taɓarɓarewar zamantakewa mai nasaba da nuna wariyar addini ko ƙabilanci ba. 

Marigayi Maitama Sule (Ɗan Masanin Kano) ya taɓa faɗin cewa, mulki na iya zama ne kaɗai a hannun shugaba nagari mai adalci. Shugaba da jama’a suke jin daɗinsa shi ne wanda ba ya nuna musu wariya, kuma ba ya bambanta wani sashi na jama’ar sa a kan wani sashi, ya ɗauki kowa daidai da kowa. 

Rashin nuna adalci da gaskiya wajen tafiyar da sha’anin mulki, shi ya ke sa jama’a kukan an zalunce su ko an danne musu wasu haƙƙoƙin su. Wannan kuma shi ya bambanta ƙaramar hukumar Toro da sauran yankuna, domin kuwa duk da rabe raben tsarin tafiyar da harkokin al’umma (da ya haɗa da ɓangaren gwamnati, ’yan siyasa da sarakuna) ba a tava samun ƙorafin tauyewa wani ɓangare haƙƙinsa ba. Wannan shi ne abin da al’ummar Toro ke alfahari da shi, kuma take ƙoƙarin ganin ta cigaba da riƙo da shi har abada. 

Toro na daga cikin ƙalilan ɗin ƙananan hukumomin Nijeriya da suka samu nasarar cin moriyar albarkacin bambancin addini da ƙabilun da ke yankin. Al’ummar yankin na zaune lafiya da junan su, duk kuwa da bambancin da ke tsakanin su. 

Wani abin ban sha’awa da ɗaukar hankali shi ne yadda yankin ƙaramar hukumar Toro ya cigaba da kasancewa cikin lumana da kwanciyar hankali duk kuwa da yadda ake samun fitintinu iri-iri da ke tasowa daga jihohin da ta ke maƙwaftaka da su na Filato da Kaduna. Ba ma wai don ganin Toro ita ce qaramar hukuma mafi girma a Nijeriya ba, a’a kasancewar ta ma yanki mafi zaman lafiya da kwanciyar hankali shi ma babban abin a yaba ne. 

Sai dai kuma, a yayin da Babban Zaven 2023 ke ƙara matsowa, ’yan bokon yankin da ke da ƙarfin faɗa a ji sun fara duba yiwuwar samar da wani wakili nagari da zai wakilci al’ummar yankin a Majalisar Wakilai ta Tarayya. Daga cikin waɗanda ake ganin za su iya amsa sunan su a wannan vangare akwai ɗan majalisa mai ci na yanzu, Honarabul Umar Muda Lawal da ke wakiltar al’ummar mazaɓar Toro a Majalisar Wakilai ta ƙasa zango na tara. 

A halin da ake ciki, wannan ɗan majalisa na nan ya duƙufa wajen ganawa da masu ruwa da tsaki na yankin da ya ke wakilta, domin tantance karɓuwarsa da kuma auna ƙoƙarin sa a wakilcin da al’ummar yankin suka tura shi ya yi a Majalisar Ƙasa. Wannan ƙoƙari da ya ke yi babu shakka shi zai ƙara nunar masa da yiwuwar samun cigaba da goyon bayan jama’ar yankin a babban zaɓe mai zuwa na 2023. Kuma kasancewar sa matashi wannan abin da ya ke yi zai taimaka masa wajen samun damar cigaba da wakilcin da ya ke yi a Majalisar Wakilai ta Tarayya. 

Bayan shi akwai wasu daban da su ma suka fita don bayyana sha’awar su ta yi takarar neman wannan kujera a ƙarƙashin jam’iyyu daban-daban da suka haɗa da jam’iyyun PDP, APC, da kuma SDP. A cikin su akwai Babban Daraktan ofishin kula da Cinikin Muhimman Bukatun Gwamnatin Jihar Bauchi, Injiniya Injiniya Titus Sanga, wanda shi ma wani tauraro ne da ake alfahari da shi. Sannan ana yi masa ganin ƙwararren da idan ya samu wannan damar zai iya kawo sauyi a siyasar Toro. An yi la’akari da haka ne ganin irin yadda ya ke tafiyar da siyasar sa ba tare da nuna wani bambanci ko wariyar wani ɓangare ba. 

Lokaci ya yi da za a kawo canji a siyasar Toro. Gaskiyar magana shi ne ya kamata a samar da wani jajirtacce da zai kawo sauyi da cigaban da zai yi tasiri wajen inganta makomar siyasar Toro da zamantakewar al’ummarta ba tare da kallon addini ko wata ƙabila ba. Ya kamata a ba da goyon baya ga mutumin da aka tabbatar da ingancin sa da ƙwarewar sa wajen ganin ya samar wa ƙaramar hukumar Toro shugabanci nagari da cin moriyar dimukraɗiyya. 

A matsayina na mai kishin samar da shugabanci nagari a ko’ina a Nijeriya, ba a ƙaramar hukumar Toro kaɗai ba, na goyi bayan ra’ayin tsohon Kakakin Majalisar Matasan Arewacin Nijeriya, wanda kuma har wa yau shi ne Shugaban ƙungiyar Matasan Jam’iyyar APC, Rt. Hon. Ukasha Hamza Rahama, da shugaban ƙungiyar matasa ta Arewa Youths Advocate for Peace and Unity Initiative Sani Ɗan Audi Mohammed waɗanda dukkan su haziqan matasa ne da suka fito daga yankin ƙaramar hukumar Toro, a Jihar Bauchi kuma suke ba da gudunmawa wajen samar da zaman lafiya da cigaban al’umma a Nijeriya, waɗanda ke ganin dalilin da ya sa ƙasar nan take cikin halin koma baya da rashin cigaba a siyasar ƙasar nan, shi ne nacewa da ake yi wajen ɗora tubalin siyasar mu a kan addini da ƙabilanci. Wannan ne kuma ya sa na ke yabawa Kwamred Aminu Saleh na Ƙungiyar Toro Youths Alive wanda shi ma ya yi yawo a ƙasar nan yana fafutukar gina aƙidar zaman lafiya da haɗin kan ƙasa, don samar da cigaba mai ɗorewa. 

A taƙaice, bayanan da na yi ta ginawa a baya na yi su ne domin nuna bayyana irin ƙwararan dalilan da na ke da su, waɗanda kuma na ke ganin za su amfani ƙaramar hukumar Toro wajen samun wakilci nagari, shugabanci mai adalci da kuma uwa uba zaman lafiya mai ɗorewa. 

Abin da na sani ne kuma na yi imanin zai kasance, duk wani ɗan siyasa da ya yi yunƙurin kawo wa al’ummar Toro a 2023 siyasar nuna wariya ko ƙyamar wani ɓangare to, babu shakka zai kwashi kashin sa a hannu. 

Zan kammala da gargaɗin duk wasu da za su yi ƙoƙarin kawo wa al’ummar Toro wani mugun ra’ayi da zai ruguza kyakkyawan tarihin da suke da shi tun iyaye da kakanni na son juna da haɗin kai su kiyayi kansu daga wannan mugun tafarkin da suke shirin jefa kansu. Tsawon shekaru yankin ƙasar Toro da al’ummar sa ya zama wajen da jama’a da dama ke sa masa ido, kuma ake kishin sa. Bai kamata mu bari wani ko wasu su zo su lalata mana wannan kyakkyawar shaidar ba. Ya kamata su ɗauki misali daga abin da ke faruwa a makwafciyar Jihar Bauchi wato Filato, inda siyasar ƙabilanci da wariyar addini ya ke jefa jihar da al’ummar ta cikin wani yanayi mawuyaci na taɓarɓarewar tsaro da zaman lafiya. 

Masu hikimar magana dai na cewa, idan gemun ɗan uwanka ya kama da wuta, sai ka shafa wa na ka ruwa. Aiki da hankali, ya fi aiki da agogo.