Sojin sama sun kai sumame dabar ƙasurgumin ɗan bindiga tare da ceto mutane 76 a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta ce sojojin sama sun kai samame, inda suka samu nasarar tarwatsa maɓoyar ɗan bindiga Babaro tare da ceto mutum 76 da aka yi garkuwa da su.

A wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida na Katsina, Nasir Mu’azu ya fitar, ya ce Babaro da yaransa ne suka kai hari a Gidan Mantau da ke ƙaramar hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina.

Ya ce, “sojojin saman Najeriya ne suka kai harin ta sama a tsaunin Pauwa da ke ƙaramar hukumar Ƙanƙara, inda suka samu nasarar ceto mutum 76 ciki har da mata da ƙananan yara.”

Kwamishinan ya ce tsaunin ne babban sansani kuma maɓoyar ɗan bindigar, inda ya ke shirya kai hare-hare zuwa garuruwa.

Sai dai kwamishinann ya ce an samu wani ƙaramin yaro ya rasu, sannan ya ƙara da cewa nasarar da suka samu na cikin yunƙurin da gwamnatin jihar ke yi wajen tabbatar da tsaro a jihar.

A ƙarshe ya yaba wa sojojin Najeriya bisa jajircewar da ya ce suna yi wajen gudanar da aiki ba tare da gajiyawa ba.

By ukarofi