
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A jiya Asabar aka fara gudanar da taron Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta 2025 a Birnin Enugu da aka saba yi a kowace shekara.
Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da ɗan siyasar Afirka ta Kudu, Julius Malema da wasu lauyoyi su sama da 20,000 suka samu halarta.
Da fari shugaban ƙungiyar, Afam Osigwe ya jagoranci dubunnan lauyoyi a wani zagayen wasa jini a titunan birnin, inda wasu da dama suka riƙa shiga sahunsu daga bisani.
Da yake ganawa da manema labarai, Osigwe ya bayyana cewa Enugu waje ne da ke da yanayi mai kyau na gudanar da ire-iren tarukan cikin walwala.
Lamarin da ya sa suka bayyana farin cikinsu duba da yadda gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Pete Mbah ta ke ƙoƙarin samar da yanayi mai kyau ga al’umma.
Haka ma lauyoyi da dama sun yaba wa gwamnatin jihar musamman akan yadda ta tsara tarbar baƙi da kuma yanayin gudanar da taron.
