Takardun kotu sun bayyana yadda direban tirela da wasu ƴan ƙasar waje suka damfari Ɗangote biliyoyin kuɗaɗe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jagoran masu kuɗin Afirka, Alhaji Aliko Ɗangote ya tsallake rijiya da baya yayin da wasu ƴan kwangila tare da wasu ƴan cikin gida suka kitsa yi masa damfarar maƙudan kuɗaɗe, kamar yadda Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayyana.

Takardun kotu da Sufeton ƴan sanda ya shigar sun bayyana yadda wata tawagar ƴan ƙasar waje suka yi yunƙurin damfarar Matatar Ɗangote kuɗin da adadinsa ya kai Dala miliyan 50.

Haka kuma wani direban tirela ya sauya akalar wasu tireloli da ke maƙare da ƙarafunan rodi na kamfanin simintin Ɗangote na wasu biliyoyin nairori.

Waɗanda ake zargin sun haɗa da He Jun, Sun Yuzhu, Yong Li, Feng, JayKumar Sagar da kuma Rajnish Gupta waɗanda dukkanin su ƴan Nahiyar Asiya ne, inda aka ba su kwangilar sanya bututun mai zuwa matatun Ɗangote a Legas.

A madadin yin aikin ne sai suka samar da takardar kammala aiki ta ƙarya, wadda suka gabatar a wata kotun Landon ta harkokin ƙasa-da-ƙasa (LCIA) da nufin mallake Dala miliyan 50.

An gano su ne a lokacin da Matatar Ɗangote ta gabatar wa kotu takardun shaidar cewa ba a kammala aikin ba, inda ta yi watsi da ikirarin tare da neman a gudanar da bincike.

A ranar Juma’a yayin sauraron ƙarar, lauyan da ke kare ɓangaren ƴan sanda, Rimamsomte Ezekiel ya shaida wa kotun cewa an shigar da ƙarar aikata manyan laifuka akan waɗanda ake zargin a Babbar Kotun Legas.

Akan haka ne ƴan sandan suka nemi a riƙe wasu asusun bankuna guda biyar da aka alaƙanta da direban tirelan, wato Tahir, bisa zarginsa da laifin sauya akalar dukiyar kamfanin attajirin.

By Babaji