Sojoji sun ceto mutane 397 yayin da ‘yan ta’adda 57 suka miƙa wuya a Yuli – DHQ

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta sanar da cewa jami’an sojoji sun yi nasarar ceto mutane 397 da aka yi garkuwa da su a lokacin atisaye daban-daban a watan Yuli, yayin da ‘yan ta’adda 57 da iyalansu suka miƙa wuya a ƙoƙarin daƙile miyagun ayyuka a sassan Nijeriya.

Daraktan yaɗa labara na hedikwatar, Manjo-Janar Michael Onoja ne ya sanar da nasarorin a ranar Juma’a yayin gabatar da sakamakon ayyukan sojoji na watan Yuli.

A cewarsa, sojoji a rassa daban-daban sun halaka jimillar ‘yan ta’adda da wasu ɓarayi guda 102, sun kama mutane 345 da ake zargi, sannan sun ƙwato makamai 59 da alburusai 1,811 a watan.

Ya bayyana cewa, a Shiyyar Arewa maso Gabas, dakarun Atisayen Haɗin Kai sun yi nasara akan ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP a sassan jihohin Adamawa, Bauchi, Borno da Yobe, wajen daƙile wasu hare-harensu.

Ya ce, sojoji sun halaka mayaƙan ‘yan ta’adda 54, sun kama 102, sun ceto mutane 102 da aka sace, sannan 57 da iyalansu sun ajiye makamansu tare da miƙa wuya ga dakarun tsaron.

Jami’in yaɗa labaran ya ƙara da cewa, a ranar 4 da 17 ga Yuli ne iyalai bakwai na wasu ‘yan ta’adda da suka tsere da yankin tsaunukan Mandara suka miƙa wuya ga sojoji a Ƙaramar Hukumar Gwoza da ke Jihar Borno.

Haka ma a ranar 25, wani babban jami’in harkokin kuɗin ‘yan ISWAP ya miƙa wuya ga sojoji a yankin hanyar Ladari zuwa Jegarawa zuwa Tunokalia da ke Gamboru zuwa Wulgo, wanda nan ne wajen da suka fi amfani da shi yayin safarar kayayyakinsu.

By Babaji

Leave a Reply