
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Alƙalin alƙalan Nijeriya (CJN), Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun ta umarci lauyoyi da jami’an kotu da su daina amfani da laƙabin ‘Barrister’ gabanin ainihin sunayensu a dukkan ayyukan da suka shafin Kotun Ƙoli a hukumance.
Manhaja ta ruwaito cewa, umarnin da ƙunshe ne a wata takarda da ke ɗauke da kwanan wata 13 ga Yuli, 2026 kuma Babban Rajistiran kotun, Kabir Akanbi, ya sanya wa hannu.
Takardar, wadda aka fitar da ita musamman don jami’an shari’a, rajistirorin kotu da lauyoyi, ta bayyana cewa umarnin ya fara aiki ne a nan take a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin biyayya ga ƙa’idojin ƙwarewar aiki a kotun.
Haka kuma, ta umarci jami’an da al’amarin ya shafa da su daina amfani da laƙabin yayin amsa wa ayyuka a hukumance da sanyawa acikin takardun ayyukan.
Domin tabbatar aiwatar da umarnin, shugabar alƙalan ta kuma umarci jami’an sanya ido daga dukkan rassa da ofisoshin kotun su tabbatar da biyayya ga dokar.
Hakan na zuwa ne makonni kaɗan da Majalisar Ilimin Shari’a ta ƙalubalanci yadda masu shirin zama lauyoyi suke amfani da hular lauyoyi da rigunansu wajen gabatar da kansu a matsayin waɗanda suka cancanta gabanin a tabbatar da su a hukumance (call to the Nigerian Bar).
A cewar majalisar, hakan na haifar wa aikin shari’a cin fuska, wanda ka iya sanyawa a hukunta waɗanda aka samu da laifin aikata hakan.
