Sojoji sun kashe ‘yan bindiga guda bakwai Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Sojoji sun kashe ‘yan bindiga su bakwai tare da gano babura na hawa guda huɗu a ƙauyen Baba da ke ƙaramar hukumar ƙankara a Jihar Katsina.

Wannan nasara da sojojin suka samu ya biyo bayan bayanai na sirri da suka samu kan yadda ƴan bindigan suka hana noma a ƙauyen Baba da ke ƙaramar hukumar.

Wannan bayanin na ƙunshe a takardar sanarwa ɗauke da sa hannun kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa.

A cewar sa bayan kwashe tsawon lokaci ana musayar wuta, sojojin sun samu nasarar kashe ƴan bindiga guda bakwai, wasu da dama kuma suka tsere ɗauke da raunuka.

Gwamnatin Jihar Katsina ta jinjina wa jami’an sojin da su kayi wannan na mijin ƙoƙari tare da jaddada ƙudirin gwamnati na cigaba da ba jami’an tsaron goyon baya don ganin an kakkaɓe sauran ƴan ta’adda a jihar.

“Gwamnatin Katsina ta hannun ma’aikatan harkokin cikin gida da tsaro zata cigaba da taimakawa jami’an tsaro ta basu bayanan sirri da shigar alamomin domin su bada ta su gudunmawa wajen yaƙi da ta’addanci a jihar,”inji kwamishinan.

Ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnati na bakin ƙoƙarin ta wajan kare rayuka da dukiyar al’umma.

By ukarofi