Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 25 da tarwatsa sansanoninsu a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

A wani sumame da dakarun rundunar Air Component Operation Fansan Yamma suka kai, sun fatattaki wasu sansanonin ‘yan ta’adda a yankin Fakai inda suka kashe ‘yan ta’adda 25 a Jihar Zamfara.

Babban jami’in hulɗa da jama’a na haɗin gwiwa na Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

A cewar sanarwar, wasu sansanonin da aka share sun haɗa da na Bello Turji da Mallam Ila, inda wasu ‘yan ta’adda sama da 18 suka samu raunuka sakamakon harbin bindiga, wanda hakan ya janyo koma baya ga ƙungiyar ta’addancin.

“Dakarun Sashe na biyu na rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Yamma Operation Fansan Yamma sun yi nasarar tarwatsa maɓoyar ‘yan ta’adda a yankin Fakai da ke ƙaramar hukumar Shinkafi dake Jihar Zamfara, a ranar 10 ga watan Janairun 2025”. A cewar sanarwar.

A cewar sanarwar, mutane bakwai da aka yi garkuwa da su, sun samu kuɓuta daga sansanonin ‘yan ta’addan a yayin farmakin.

Laftanar Kanar Abubakar ya ci gaba da cewa, farmakin na Fansan Yamma zai ci gaba da bibiya tare da kakkaɓe duk wasu ‘yan ta’addan da ke yankin.

“Saboda haka muna gargaɗin dukkanin jagororin ‘yan ta’adda da abokan su da su miƙa wuya tare da yin watsi da tashin hankali ba tare da wani sharaɗi ba, yayin da sojojin mu ke ci gaba da ƙoƙarin kawar da duk wani nau’in ta’addanci”.

Sojojin sun bai wa jama’a tabbacin su na jajircewa wajen dawo da zaman lafiya da tsaro a cikin al’ummomin da lamarin ya shafa.