Sojojin 17 brigade sun ceto mutane 84 daga hannun ‘yan bindiga a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Haɗin gwiwa na sojojin sama da na 17 brigade sun sami nasarar ceto mutane 84 a hannun ‘yan bindiga a ƙaramar hukumar ƙanƙara.

‘Yan bindigan sun mamaye ƙauyukan Malori da Matalawa a yankin ƙanƙara ƙarƙashin jagorancin ƙasurgumin ɗan ta’adda
Sanusi Dutsinma da ya kafa sansani a Dutsen Pauwa da ke yankin ƙanƙara.

A wata takardar sanarwar ɗauke da sa hannun kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa ya ce da sojojin suka sami bayanan sirri na mamayen nan take suka tunkaro ƙauyukan.

“An dai ta ɗauki bada daɗi tsakanin ‘yan bindigan da sojoji a ƙauyen Malori da Matalawa inda ‘yan bindiga suka mamaye,sai dai sojojin suka sami galaba a kan ‘yan ta’addan”inji Dakta Ɗanmusa.

Ya bayyana cewa sojojin sun sami nasarar ceto mutane 84 a yayin da suka kashe ‘yan bindiga uku wasu da yawa suka gudu suna ɗauke da manyan raunuka.

Kwamishinan ya sanar da cewa cikin mutanen da aka ceto sun haɗa da maza bakwai, mata 23 sai ƙananan yara 54 da yanzu haka suna hannun gwamnati ana kula da su .

“Nan bada jimawa ba da zarar an kammala duba lafiyar su,za a miƙa su ga iyalan su”inji Dakta Ɗanmusa.

Ya yaba da ƙoƙari da ƙwarewa da sojojin suka nuna wajen fatattakar ‘yan bindiga ba tare da wani soja ya jikkata ba .

Dakta Nasiru Mu’azu Ɗanmusa ya dangantaka wannan nasara da sojoji tare da sauran jami’an tsaro ke samu na yaƙi da ta’adanci a jihar da ba zai rasa nasaba da irin yadda gwamnatin Dikko Raɗɗa ya tashi tsaye wajan kawo ƙarshen ta’adanci a jihar.

By ukarofi