Nijeriya ta faɗo mataki na 105 a jaddawalin farin ciki na duniya

Spread the love

Najeriya ta faɗo zuwa matsayi na 105 daga cikin ƙasashe 147 a jadawalin farin ciki na duniya na 2025, wanda aka fitar ranar Alhamis yayin bikin Ranar Farin Ciki ta Duniya. Wannan ya nuna cewa Najeriya ta ragu matsayi uku daga na 102 a shekarar 2024. Duk da haka, Najeriya ta zama ƙasa ta 10 mafi farin ciki a nahiyar Afirka. 

Libya ce ta kasance ƙasa mafi farin ciki a Afirka, tana kan matsayi na 79 a duniya, duk da ƙalubale masu yawa da ƙasar ke fuskanta. 

A matakin duniya, Finland ta ci gaba da zama ƙasa mafi farin ciki a duniya karo na takwas a jere, tare da sauran ƙasashen Nordic kamar Denmark, Iceland, da Sweden suna biye mata. 

Ƙasashen da suka fi farin ciki a duniya sun haɗa da: 

1. Finland 

2. Denmark 

3. Iceland 

4. Sweden 

5. Netherlands 

6. Switzerland 

7. Norway 

8. Israel 

9. Luxembourg 

10. New Zealand 

A gefe guda, Amurka ta kasance a matsayi na 24, yayin da Birtaniya ke matsayi na 23, duk da cewa sun fuskanci raguwa a cikin farin ciki a cikin ‘yan shekarun nan. Kanada kuwa na cikin ƙasashe 20 mafi farin ciki, tana matsayi na 18. 

A wani ɓangare kuma, Afghanistan ta ci gaba da zama ƙasa mafi bakin ciki a duniya a matsayi na 147, yayin da Saliyo ke matsayi na 146, Lebanon na 145, Malawi na 144, da Zimbabwe na 143. 

Rahoton Farin Ciki na Duniya na Majalisar Ɗinkin Duniya yana bibiyar farin ciki ta amfani da abubuwa guda shida: tattalin arziki, tallafi na zamantakewa, tsawon rayuwa mai lafiya, ‘yanci, karimci, da fahimtar cin hanci da rashawa. Wannan shekarar rahoton ya mai da hankali ne kan tasirin kulawa da taimako ga farin cikin jama’a.

By ukarofi