Sojojin Nijeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram da suka yi ƙoƙarin kutsawa sansaninsu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar sojin Nijeriya ta ce sojojinta na Operation Haɗin Kai sun daƙile wani yunƙurin kai hari da ‘yan Boko Haram da ISWAP suka yi a sansanin sojojin ruwa da ke Tafkin Chadi, a yankin Fish Dam, inda suka halaka da dama daga cikin su a wani samame na haɗin gwiwa.

Rundunar ta faɗi hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a shafin sada zumuntarta na X.

Sanarwar ta ce mayaƙan Boko Haram ɗin sun fara harin ne da misalin ƙarfe 2 na dare, da nufin lalata sabbin motocin ruwa na musamman da gwamnatin Jihar Borno ta tanada domin share hanyoyin ruwa a Tafkin Chadi.

Sai dai ƙoƙarinsu ya ci tura, domin sojojin ruwa a sansanin Tafkin Chadi sun yi musu kwanton-ɓauna tare da samun ƙarin goyon baya daga sansanin Baga.

“An samu musayar wuta mai tsanani tsakanin sojojin da ‘yan Boko Haram ɗin har na tsawon sama da sa’o’i biyu, inda daga ƙarshe suka janye ba tare da cimma burinsu ba kuma sojojin sun samu nasarar halaka da dama daga cikin su tare da ƙwato wasu makamai da na haɗa bom,” inji sanarwar.

Sanarwar ta kuma ce a yayin harin, mayaƙan sun samu damar lalata wasu kayayyaki guda uku ciki har da motar ɗaukar marasa lafiya da wasu motocin aiki biyu.

Haka kuma, wasu dakarun rundunar sun samu raunuka a lokacin musayar wutar.

By ukarofi