Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Hukumar Kula da Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano wato Science and Technical Schools Board STSB, ƙarkashin shugabancin Farfesa Dahiru Sale Muhammad ta shiryya taron sanin makamar aiki ga shugannin makarantun sakandare da mataimakansu da jami’an kula da shirya jarabawa na makarantun hukumar ta STSB domin zurfafa ilimim sanin aiki domin cimma nasara da wananna hukumar ta sa gaba ako da yaushe na bunƙasa ilimin kimiyya da fasaha kamar yadda Gwamnnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf yake da himma na ganin al’ummar Kano ta zama ta ɗaya a fanin ilimi ako da yaushe wanda wannan ce ta sa gwamnan ke zama kan gaba a gwamnonin Nijeriya wajan ba ilimi kaso mafi tsoka a shekarar bara ya bada kashi 30 cikin 100 bana kuma kasafin kuɗinsa ya samu kashi 31 cikin 100 wanda shi ne gwamna na farko a kano da Najeriya da ke ba ilimi Mahimmanci a kasafin kuɗinsa duk shekara kamar dai yadda shugaban hukumar STSB Farfesa Dahiru Sale Muhammad ya bayyana bayan kammala horar da shugabannin makarantin da aka yi a ranar Talatar da ta gabata a ɗakin taro na gidan gwamnatin Kano.
Haka kuma Farfesa Dahiru ya yaba wa ɗaukacin Darktocin STSB da ɗaukacin maaikatan hukumar kan irin goyan baya da haɗin kai da su ke bayarawa wajen cigaban wannan hukuma inda kuma ya hori mahallata wannan horo na yini ɗaya na sanin makamar aiki da suyi aiki da abunda aka horar da su domin shi ne zai bada kyakykyawan sakamoko wajen samun ingantaccen ilimi kimiyya da Fasaha da kuma tarbiyyar ga ɗaliban da suke kula dasu a waɗannan Makarantu na kimiyya da Fasaha a Kano
A ƙarshe ya yi amfani da wannan dama wajen nuna godiyar sa ga Allah Maɗaukakin sarki na ganin lokaci da Gwamna ya ke bunƙasa ilimi da cigaban Kano ta kowanne fanni Musamman wajen raba kayan makaranta ga ɗaliban Firamare sama da Dubu 800 a ƙananan hukumomin Kano 44 a dai dai lokacin da Alhaji Abba Kabir Yusif ya cika shekaru 62 a duniya masu albarka.