Sufeto-Janar ya tura CP Usaini Gumel zuwa Kano a matsayin Kwamishinan’Yan Sandan jihar

Daga WAKILINMU

Sufeto-Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya, Usman Alkali, ya sake soke tura wani Kwamishinan ‘Yan Sanda zuwa Jihar Kano.

IGP Alkali ya soke tura Feleye Olaleye a matsayin Kwamishinan ‘Yan Sanda a Kano, kana ya maye gurbinsa da CP Ahmed Kontagora.

Sai dai kuma, a wata sigina ta daban da rundunar ta ƙasa ta aike ta nuna yanzu IGP Alkali ya tura CP Usaini Gumel a matsayin Kwamishinan da zai jagoranci rundunar a Kano yayin zaɓen gwamnoni da ke tafe a jihar.

A ranar 8 ga Maris IGP ya soke tura CP Balarabe Sule a matsayin wanda zai maye gurbin CP Mohammed Yakubu a jihar bayan da jam’iyyar hamayya ta nuna rashin yardarta a kan haka.

Takardar sigina ɗin mai lamba TH.5361/FS/FHQ/AB3/SUB.6/146, ta kuma nuna IGP Alkali ya tabbatar da wasu ƙananan sauye-sauye a tsakanin jami’an rundunar ‘yan sanda.

Inda ya ba da umarnin a yi canjin gurbin aiki tsakanin DCP Auwal Musa da DCP Nuhu Darma a matsayin mataimakin Kwamishina mai kula da ayyuka da kuma Sashen Binciken Manyan Laifuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *