
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles ta yi nasarar doke Reggae boys na ƙasar Jamaica, inda ta lashe kofin gasar Unity Cup da aka yi a Ingila, ranar Asabar.
Moses Simon na Nijeriya shi ya fara zura ƙwallo a minti na 9, a yayin da Dixon na Jamaica ya farke a minti na 12.
Daga bisani Samuel Chukwueze a minti na 53 ya ƙara ƙwallo a raga, inda minti goma bayan haka ne sai Russell ya farke wa Jamaica a karo na biyu.
Bayan tashi a haka ne sai aka yi bugun fenareti, wanda ya bai wa Nijeriya nasara da ci 5 da 4.
