Tumsah ya tallafa wa ɗaliban JAMB 29 da N2.9m a Yobe

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMIN Damaturu

A ƙoƙarinsa na ƙarfafa wa matasan Jihar Yobe gwiwa a fannin ilimi; Barista Kashim Musa Tumsah (KMT), ya tallafawa ɗalibai 29 waɗanda suka samu maki 300, ko fiye da haka a jarrabawar share-fagen shiga jami’a (JAMB) na bana.

Lokacin da take jawabi a madadin Barista Kashim Musa Tumsah, Hajiya Adama Balla ta bayyana cewa kowane ɗalibi ya samu kyautar ₦100,000, wanda ya kai jimillar Naira Miliyan 2.9 ,wannan shi ne karon farko wanda wani mutum ɗaya ya baiwa ɗalibai tallafi makamancin wannan a jihar.

Taron bayar da tallafin ya gudana a babban ɗakin taron ƙungiyar ƴan jaridu ta ƙasa (NUJ) dake Damaturu, babban birnin jihar, wanda ya samu halartar jami’an gwamnati, iyaye, da shugabannin al’umma, a ranar Asabar.

Tumsah ya bayyana cewa, ya aiwatar da wannan tallafin ne don goyon bayan ƙoƙarin gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni, biyo bayan ayyana dokar ta ɓaci a fannin ilimi, wanda hakan ne ya bayar da damar samun sauye-sauye da ingantattun manufofi masu kyau.

Ya ce, ta hanyar waɗannan muradu na ƙoƙarin tabbatar da cewa kowane yaro namiji ko mace, ko masu fama da nakasa su ke da cikakkiyar damar samun ilimi mai inganci.

“Shigar ku a manyan makarantu ba ya na nufin shi ne kaɗai nasarar ku ba; face kawai wata shaida ce wadda za ta ba ku juriya. Saboda nakasa ba ta nufin rashin samun dama ba ce, kuma waɗanda suka dage wajen yin nasara a yau sun tabbatar da hakan.” In ji shi.

“Saboda idan aka ilimintar da mace, hakan zai bata zarafin canza iyalinta, da ma al’ummarta, da ƙasa baki ɗaya. Kuma babu wanda zai ce muku ba ku cancanta ba a tafarkin neman ilimi ko ɗakunan gwaje-gwajen kimiyya, ko shugabanci.”

A nashi jawabi, a madadin iyayen ɗalibai, ɗan majalisar dokokin Jihar Yobe, Hon. Kachala Maina, mai wakiltar ƙaramar hukumar Machina, ya yaba wa da ƙoƙarin Barista Kashim Musa Tumsa, bisa ga wannan tallafi ga harkokin ilimi a Jihar Yobe, inda ya yi kira ga masu hannu da shuni da sauran jama’a, su yi koyi da irin wannan aikin gina al’umma.

By ukarofi