Cikar shekaru biyu: Tinubu ya ƙaddamar da zangon farko na babban titin Legas zuwa Kalaba da wasu ayyuka

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta cigaba da inganta al’amuran ƙasa da amfani da fasahar zamani gami da inganta al’umma a yayin da ya ƙaddamar da zangon farkon na aikin babban titin ‘Lagos-Calabar’ da wasu muhimman ayyukan tituna a ƙasar.

A yayin taron ƙaddamarwar a Legas ranar Asabar ne Shugaba Tinubu ya umarci Ministan Ayyuka, Dave Umahi da wasu ministoci da su sanya ido akan ayyukan tituna a faɗin ƙasar don tabbatar da an bi dokoki da tsare-tsaren aikin.

Ya ce, gwamnatin ba za ta sake biyan diyya ga kamfanonin gine-ginen tituna da ba su cike ka’idodin doka ba, yana mai nuna muhimmancin raya birane da kiyaye bin doka da oda.

Shugaba Tinubu ya kuma lallashi al’ummar Nijeriya game da halin da ƙasar ta ke ciki, inda ya ce su ƙara haƙuri da gwamnatin a yayin da ta ke ƙoƙarin daidaita al’amarun ƙasar.

Ya kuma yi godiya ga ministan ayyuka da ƴan kwangila da ɗaukacin al’ummar Nijeriya musamman ƴan Legas, waɗanda suke goyon bayan ayyukan, yana mai kira a gare su da ɗore akan haka domin amfanin su da ma ƙasa baki ɗaya.

Ga rahoton ayyukan da Shugaban ƙasar ya ƙaddamar kamar yadda Blueprint ta ruwaito:

“The projects commissioned by the President in the South-South region are the rehabilitation of Calabar-Ugep-Katsina-Ala Road Section II (Ugep-Katsina-Ala) in Benue/Cross River States, dualisation of East-West Road Section II (Sub Section I) Eleme Junction in Port Harcourt – Ahoada in Rivers State; rehabilitation of Alesi-Ugep(Iyamoyung-Ugep) Section in Cross River State. Upgrading of 15km Section of the East-West Road Port Harcourt (Eleme Junction)-Onne Port Junction in Rivers state.”

“President Tinubu commissioned the rehabilitated Enugu-Port Harcourt Road Section III, Enugu-Lokpanta, in the South East Zone, a new bridge at Akpoha in Ebonyi State to replace the near-collapsed bridge; reconstruction of the collapsed Enugu Bridge at New Artisan Market Enugu-Port Harcourt Road in Enugu state.”

“Other commissioned projects in the South West Zone are: Rehabilitation, Construction & Expansion of Lagos-Shagamu-Ibadan Dual Carriageway Section II in Oyo state; rehabilitation of Ikorodu-Shagamu road in Lagos state; emergency comprehensive repair of the Eko Bridge (4.1km) in Lagos state (from Alaka, Surulere-Apongbon including all Ramps); the construction of Deep-Sea Port Access Road in Lagos state through Epe to Shagamu – Benin Expressway in Lagos and Ogun states.”

“In the North Central zone, President Tinubu commissioned the construction of the Shendam Bridge in Plateau state and the Ilobu-Enrile road in Kwara and Osun states.”

“In the North East Zone, he commissioned the Jimeta Bridge in Yola, Adamawa state.”

“In the North West Zone, he commissioned the reconstructed Yakasai Badume-Damargu-Marken Zalli roads in Kano state and the reconstruction of Kano-Kwanar Danja Hadeja Section II: Kano-Tsalle in Kano and Jigawa state.”

“President Tinubu flagged off the following new projects: Ibadan-Ife-Ilesha-Akure-Benin road in Oyo, Osun, Ondo, and Edo states; construction of Nembe-Brass road; construction of a section of Enugu-Onitsha Carriageway (total length of 107km); and rehabilitation of Zaria-Hunkuyi-Kufur-Gidan Mutum Daya road in Kaduna/Kano states.”

“Also, the President flagged-off the dualisation of Kano-Maiduguri road, linking Kano-Jigawa-Bauchi-Yobe and Borno states (Section I: Kano-Wudil-Shuarin), which has a Total length of 105km; the construction of Kano Northern Bypass road in Kano state; and the construction of Maiduguri Bypass road”, kamar yadda ta wallafa.

By Babaji