Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Dakta Salihannur Adam, shugaban Gidauniyar Salihannur Charity Foundation ta ƙasa mai babban ofishinta a Kano, ya bayyana cewa babu wata hanya da mutum zai samu arziki mai yawa cikin ƙanƙanin lokaci kamar taimaka wa mabukata saboda Allah.
Shugaban gidauniyar ya bayyana hakan ne a wajen taron rabawa mata sama da 300 tallafin jari da kayan sana’o’i, bayan an koyar da matan sana’o’in zamani da na gargajiya. Gidauniyar Alhaji Ibrahim S. Linda Foundation ce ta shirya taron ranar Asabar da ta gabata.
Dakta Salihannur, wanda kuma shi ne shugaban cibiyar binciken ganyayyaki, bishiyoyi, tsirrai, sauyoyi da ciyayi da sarrafa su domin magance cututtukan da ke damun ɗan Adam, wato Salihannur Traditional Herbal Medicine da ke Kano, ya bayyana hakan ne lokacin da ya miƙa kuɗi naira dubu 500 ga shugaban gidauniyar S. Linda Foundation ta Kano.
An gudanar da taron ne a Kwalejin Nazarin Shari’a da Addinin Musulunci ta Aminu Kano, wadda aka fi sani da Legal.
A ƙarshe, ya ƙara da cewa akwai wani darasi da duk wanda ya gane shi zai samu arziki mai yawa kuma ya zauna lafiya. Ya ce darasin shi ne: “Ka ba wanda ya fi ƙarfinka a kan abin da ya fi ƙarfinka, kai ma sai Ubangiji ya ƙarfafa ka a hannun waɗanda suka fi ka ƙarfi.”
Ya ce Ubangiji ne kaɗai ke ƙarfafa mutum, kuma yana sane da duk kyautar da mutum ya yi. A cewarsa, cikin sa’o’i kaɗan Ubangiji kan nuna wa bawa alherin da ya aikata.
Ya ƙara da cewa bai kamata mutum ya yi gwaninta idan ya tallafa wa mabukaci da abin da Allah ya hore masa ba. Ya ce duk wanda bai fahimci wannan darasi ba, ya gwada yin kyauta da ikhlasi domin ya ga sakamakonta.
