Tarihin Ƙasar Bauchi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kafin mu ji asalin Bauchi, za mu fara ne da sanin Sarkin Bauchi Yakubu, wanda sunansa ya fi shahara tare da na ƙasar ta Bauchi.

An ce a ƙarni na goma sha takwas daf da soma yaƙin jihadi a ƙasar Hausa, wasu malamai biyu masu suna Mallam Adamu da Mallam Isyaku suka tashi daga Borno zuwa Ganjuwa, inda suka zauna ƙarƙashin kulawar sarkin garin na wasu ɗan shekaru.

Bayan nan sai suka tashi suka koma Kufu da zama, daga nan kuma sai suka ƙarasa Jetar.

A nan Jetar ne Mallam Isyaku ya yi abota da wani mutum da ake kiransa da suna Daɗi. Shikuwa yana zaune ne a wani wuri da ake kira Tirwin.

Mallam Isyaku ya kan ziyarci abokinsa Daɗi a Tirwin, sai rannan Mallam Isyaku ya tafi wirin Daɗi inda ya tarar da shi tare da yaron sa mai suna Yakubu.

Bayan sun gaisa sun soma firar duniya, sai Daɗi ya ce masa, “wannan yaro da ka gani da ne gareni, kuma shi ne idanuna, Allah kuwa ya sanya sonsa da yawa cikin zuciyata. Ina da kaka da yawa ban da shi amma ina so Allah ya albarkace shi a inda ya ke duka. Yanzu kuwa na baka shi, ka zama uba da shugaba a gare shi, shi kuma ya zama ɗanka mai-yi-maka hidima, domin ya sami albarkarka. Inda kake so duka ka tafi da shi, dukkan abin da ka ke so ya yi ma ka duka ka sanya shi ya yi, domin kuwa ɗanka ne, kai ne mahaifinsa.”

Abin da aka yi kenan. Mallam Isyaku ya tafi gidansa tare da Yakubu ya cewa matar sa ‘Ga ɗanki nan’.

Duk inda Mallam Isyaku za shi Yakubu na tare da shi, suna cikin haka har labarin Shaihu Usmanu ɗan Hodiyo ya zo musu. Mallam Isyaku ya tafi tare da Yakubu zuwa wurin Shehu Usmanu, ya zauna a can shekara da Shekaru yana karatun ilim.

Rannan sai Mallam Isyaku ya yi niyyar tafiya ganawa da iyalinsa, amma baya da niyyar jimawa a can. Don haka ya tsammaci cewar idan ya tafi da Yakubu zai hana shi dawowa da sauri, hakan ya sa ya shaidawa Shaihu Usmanu muradinsa tare da barin Yakubu a hannunsa. Daga nan sai ya yi wa Yakubu bayani sannan ya tafi.

Allah da ikonsa, sa’ar da Mallam Isyaku ya riski wani gari mai suna Yalwan ɗan Ziyal da ke ƙasar Kano, sai cutar ajali ta ka ma shi, a nan ya rasu. Don haka sai Yakubu ya cigaba da zama wurin shehu yana karatu, ya zama tamkar da a gidan shehu. Har ma shehu ya aurar masa da ɗiyar abokinsa Mallam Bazamfare watau Yaya.

Sa’ar da lamarin Shehu Usmanu ya bayyana, mutane suka taru a wurinsa har suka yi yawa, sai sarakunan Hausa suka fara fushi da hakan, suka zama masu fitinar jama’ar Shehu Usmanu, suna aike musu da hari, suna kisa da kame su gami da sayarwa a matsayin bayi.

Da wannan abu ya tsananta sai jama’a suka yi wa Shaihu mubaya’ar yaƙi, suka soma gina ramin ganuwa da ɗaura tuta.

A nan ne Shehu ya Umarci Yakubu ya koma gidasa Bauchi ya kira jama’arsa zuwa biyayya ga Shaihu.

Yakubu ya tashi ya tafi ga mutanensa a Bauchi da ake kira Gerawa, ya kiraye su amma basu amsa kira ba. Sai waɗansu mutane daban ne suka amsa, a cikin su akwai Mallam Adamu, da Ibrahimu, da Abdun-Dumi, da Hassan, da Faruku, da Muhammad Kusu, da Muhammad Yaro, da Hammada, da Mallam Badara, da waɗansun su da dama.

Yakubu ya ja taron jama’arsa zuwa wani wuri da ake kira Warunje ya zauna, sannan ya tashi zuwa Inkel, mutane na ta zuwa wurinsa a hankali suna yi masa mubayi’a.

Daga nan sai ya shirya yaƙi zuwa wani gari da ake kira da suna Kanyallo, ya ya ke su ya yi galaba akansu, ya ƙone gidajensu ya washe dukiyarsu, sannan ya koma wurin zamansa. Wannan kuwa shi ne farkon yaƙinsa.

Bayan wannan sai ya ƙara shirya wani yaƙin, inda ya sarauta Galadima Faruku a matsayin Sarkin Yaƙi sannan ya aike su zuwa Miri, da zuwan su kuwa sai suka faɗa musu da yaƙi.

A nan ma suka ƙarƙashe mutanen Miri, suka kamo dadansu, suka rushe gidajensu, Sarkin su ya gudu, ya tura iyalan gidansa cikin kogon dutse sannan ya ƙarƙashe su, daga bisani kuma ya kashe kansa.

Galadima Faruku ya komo wurin Yakubu da ganimar yaƙi mai yawa cikin murna da farin ciki. Daga nan sai Yakubu ya shirya wani yaƙi zuwa Gubi.
Su kuwa mutanen Gubi an ce Kafirai ne masu girman kai, gasu jaruman gaske masu ƙarfin rai, babu mai iya samun su.

Haka kuma suna zaune ne a wani wuri mai yawan duwatsu da wuyar shiga saboda santsin wurin shigar da kuma Kafe-Kafe gami da Kayoyi.

Amma duk da haka, sai da Yakubu ya ci galaba akan su. Ya kore su su ka bar gidajensu zuwa cikin duwatsu, shikuwa ya shiga cikin gidajen nasu, ya kashe na kashewa, ya kama na kamawa. Sannan ya koma gida Inkel cikin aminci da nasara.

Ai kuwa wannan yaƙi shine ya tsoratar da dukkan kafiran Ƙasar Bauchi, musamman mazauna saman duwatsu.