Amfanin zoɓorodo ga iyali

Daga BILKISU YUSUF ALI

Tambaya:
Salamu alaikum. Anti Bilkisu, muna son mu ji amfanin zoɓorodo ga lafiyar iyali.

Amsa:
Wa alaikums salam. Zoɓorodo ko zoɓo sanannen ɗan itace ne da ake sarrafa shi a rayuwar yau da gobe. Babu shakka da an ambaci zoɓorodo mutane da dama sun ɗauka kawai ana shan sa ne saboda daɗin ɗanɗanonsa, ƙalilan ne ke tunanin ana amfani da shi don magani. Zoɓorodo bayan sarrafashi don sha ana amfani da shi don magance larurori da daman gaske. Samun zoɓo cikin sauƙi musamman a arewacin Najeriya zai taimakawa mutanenmu musamman na Arewa suna da damar amfanuwa da shi. Akwai sinadarai da daman gaske a cikin zoɓorodo wanda suke inganta lafiyar ɗan adam daga ciki akwai “citric acid” da Bitamin A da Bitamin B da Bitamin C da Bitamin B2 da Bitamin B3 da ‘Sodium’ da sauransu.

-Ana amfani da zoɓo, don magance larurar da ta shafi jini kamar masu matsalar hawan jini in suka samu zoɓo suka sha yana saukar da hawan jini. Ana tafasa shi ya dahu sosai sai a tace ake sha aƙalla sau biyu zuwa uku a rana. Ana iya tafasa shi da kokwamba da citta a dai ɓangaren hawan jini.

-Shan zoɓo yana yin riga-kafi na ciwon jeji da hana wasu sinadaren na jejin yin tasiri a cikin jiki. Ana shan sa ne bayan an tafasa shi an bar shi ya huce.

-Yana magance kasala da ƙiba in ana shan sa amma ana ƙara zuma mai kyau da kanumfari.

-Ga wanda yake cin abinci amma cikinsa yana cushewa shi ma idan ya samu zoɓo ya tafasa ya sha bayan cin abinci yana taimakawa uwar hanji wajen narkar da abinci.

-Ana shan zoɓo don magance matsalar Olsa. Amma shi ana haɗawa da garin habbatus sauda da furen Albabunaj a tafasa su tare, in za a sha sai a ƙara zuma a cuɗe . Yin haka na magance larurar Olsa sosai in sha Allahu.

-Ga mai larurar ƙarancin jini in har zai dimanci shan tafasasshen zoɓorodo a ƙalla sau uku a rana in sha Allah za a samu waraka.

-Ga maza da suke da ƙarancin maniyyi shan tafasasshen zoɓo da aka tafasa da citta yana ƙara kuzarin namiji da yawaitar maniyyi.

-Yana da fa’ida shan zoɓo musamman don inganta garkuwar jiki in aka hada shi da citta da kanumfari da goriba. Zai bayar da nishaɗi da ɗanɗano sannan kuma a hannu guda kuma ya inganta tare da bunƙasa garkuwar jiki.

-Zoɓo yana maganin cholesterol yana ƙone shi a cikin jini.

-Yana ba da kariya kan cuce-cucen zuciya.

Ga mai neman ƙarin bayani ya turo saƙon tes a wannan layin ko ta whatsup 07088683334 ko a duba shafin Facebook na Bilkisu Yusuf Ali.