Yajin aiki: Ko a jikinmu don jami’o’i sun ci gaba da zama a rufe – ASUU

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU a taƙaice ta ce, lamarin bai ɗaɗa ta da ƙasa ba don jami’o’in Nijeriya sun ci gaba da zama a kulle, tana mai cewa ba za ta buɗe jami’o’in ba har sai gwamnati ta yi abin da ya dace domin gyara harkar ilimi da walwalar ma’aikata da ɗalibai.

Ƙungiyaor ASUU reshen shiyyar Kalaba wadda ta ƙunshi jihohin Akwa ibom, Cross Riba, Abia da Ebonyi, ita ce ta yi waɗannan kalaman a wata sanarwar da fitar kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Yayin zantawarsu da manema labarai shugaban ASUU na shiyyar, Aniekan Brown ya ce, “Ya zama wajibi mu jawo manema labarai domin bayyana matsayar ASUU kan batutuwan da ake kai ruwa rana da suka haɗa da yarjejeniyar da Gwamnatin Tarayya da ASUU suka cimma a 2009 da batun tsarin biyan albashi na bai ɗaya, wato IPPIS da kuma UTAS.”

Ya ci gaba da cewa, “Gwamnatin Tarayya ba ta damu ba da yunƙurin raunata abun da muka ƙirƙira a gida. Domin share tantama tsarin IPPIS da gwamnati ta kawo bai dace da tsarin jami’a ba.

“Bisa jajircewar ASUU kan ƙin yarda da IPPIS, gwamnati ta ƙalubalanci mu zo da wata hanyar mafi dacewa. ASUU ba ta yi ƙasa a guiwa ba duk da ƙuncin da aka shiga na Korona da sauransu, muka samar da UTAS.”

Ya ƙara da cewa, amma abin takaicin sai gwamnati ta sake ɓullo da wani abu na daban ta hanyar kawo wasu matsaloli na daban.

Ya ce da ma dai sun yi hasashen amincewa ko akasin haka tun da gwamnati ta ce za ta aiwatar da gwajin sahihanci a kan UTAS.

“Da ma mun yi hasashen haka sakamakon zai kasance, duba da barazaanr tsunduma yajin aiki da ƙungiya ta yi a lokacin.

“Duk da samun kaso mafi tsoka da UTAS ya yi, amma sun yanke hukunci cewa ya faɗi a gwajin da suka ce sun gudanar.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *