Rayuwar gidan Pako (2)

Manhaja logo

Assalam alaikum. Da fatan duk muna lafiya. Allah ya albarkaci jaridar Blueprint Manhaja.

Waye sarki a gidan Pako? Gidan duk da cewa babu ruwan hukuma da wurin, amman hakan bai hana cewa babu doka ba. Akwai shugaba wanda ake masa laƙabi da Bale, ko shugaba, akwai kuma faɗa wa masu taka masa baya. To sune ma masu hukunci. Mafi yawan su jahilai ne, kuma mashaya, koda kuwa za su yi hukunci to ba ruwan su da waye kai, sannan daga ina ka fito. Hukuncin su kamar hukuncin zaki ne wanda ke fama da yunwa na kwana 7, sannan yaga zebra mai ciki. Domin ko wane ne shi zai ɗanɗani kuɗa. Duk da cewa mafi yawan su mashaya ne, ko jahilai ne, gaskia idan wani ya kai ƙararka wajen su, koda kuwa baka da laifi to zaka bugu. Wani hukunci da suka taɓa yi, wani suna zama ɗaki ɗaya, ya ajiye waya yaje wanka, kan ajima kaɗan, yana dawo wa yaga ba waya, ya yi musu magana cikin ruwan sanyi sun qi, kowa yana ta ranstuwa bashi bane ya ɗauka. Ana cikin haka sai ya gaya ma hukumar gidan Pako, su kuma suka kwaso ’yan ɗakin nan, aka ɗaɗɗaure su, intakaita muku ɗaurin Boko Haram aka musu. Saboda yawan duka, har ta kai ga duk cikin su jini. Wani hukuncin kuma, Pasto ya saci kazan maƙota, bayan aka gano, sai aka ɗura masa fiffiken kaza a baki, sannan aka yi yawo da shi a jikin garin pako kowa yana masa dariya. Haka wani shima ya saci janarato, sannan aka sa shi ya daga Janaretan ɗin, ana masa bulala yana yawo. Kai bama iya wannan ba, rayuwar gidan pako nafa haɗarin da, in mai karatu ya gani da ido hawaye kawai zai riqa fitowa a idanuwan sa.

In kaga ’yan sanda a gidan pako, to in ma ya ce shan giya, ko ya je karvar cin hanci, domin ko ’yan sanda na kwarai ya shiga pako ba lale bane ya fito lafiya ba.

Maganar kasuwanci, za ka iya tara sama da Miliyan 10 a gidan pako in kana so, sannan zaka iya yin shekaru 10 a gidan ba tare da kana maganin dubu 1 ba. Haka rayuwar ta ke, kasuwanci na tafiya fiye da yadda ba ka tsammani, domin saboda kasuwanci ne ma, mafi yawan masu gida a Legas na barin gidajensu, amman su zo suna kasuwanci a gidan. Ana sayar da kaya da daraja, sannan komai na tafiya yadda ya kamata. Duk wani abinda ka sani na kasuwanci akwai shi a pako, sannan duk wani abinda ka sani na karatu akwai shi a wurin.

Gidan pako ba ruwan su da addininka, in ma ka so ka bi musulunci, ko Kiristanci, ko ka ƙi bin ko wani addini to ba ruwansu. Kai in ta kai ta muku, mafi yawan masu zama a gidan bako, tin daga koya garin su suna ajiyar kayansu, da zarar an shiga pako to sabon addini za a yi. A gidan Pako ne zaka ga liman na yi wa karuwai addu’ar Allah kawo kasuwa, fasto ya kwana yana ibada gobe ka ganshi a ɗakin karuwai. Sannan idan ma a ce maganar Allah da gaske ɗin za a bi, to ka kwana kana kira babu mai amsawa. A masalaci zaka ga bayan sallah ana karta, ko a coci kaga ana alfahasha.
Wassalam.

Saƙo daga Mohammed Albarno. O8034400338, [email protected]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *