Taron FUDMA: Yadda Alan Waƙa ya zama abin nazarin manyan malaman jami’a

Spread the love

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga AISHA ASAS 

Me ya sa wannam taron ke da muhimmanci ga adabin Hausa?

Bisa sanarwar da aka fitar, taron FUDMA bai tsaya ga nazarin waƙoƙin ALA kaɗai ba. An tsara tattaunawa kan ginshiƙan falsafar waƙoƙinsa, jigogin ayyukansa, dabarun gina waƙa, ɗabi’a, addini da kuma yadda al’adun Hausawa suka bayyana a cikin rubuce-rubucensa.

An kuma tsara gayyatar manyan masana daga jami’o’i daban-daban domin gabatar da muhimman takardun bincike.

Daga cikin waɗanda aka bayyana a matsayin masu gabatar da manyan takardu akwai Farfesa Ibrahim Aliyu Muhammad Malumfashi na Jami’ar Jihar Kaduna, Farfesa Salisu Garba Kargi na Jami’ar Ahmadu Bello da Farfesa Ousseina D. Alidou ta Rutgers University da ke Amurka.

Haka kuma, an tsara wasu muhimman abubuwa da za su gudana tare da taron, ciki har da ƙaddamar da Cibiyar Nazarin Harshen Hausa, Tarihi, Abubuwan Tarihi da Adana Takardun Dijital.

An kuma tsara bayar da kyaututtuka ga waɗanda suka yi nasara a gasar rubuce-rubucen adabi kan matsalar rashin tsaro a Arewacin Nijeriya, tare da ƙaddamar da wani littafi da ya ƙunshi gajerun labarai 30 da aka zaɓa.

Wannan ya nuna cewa an tsara taron ne a matsayin wani dandali na bunƙasa bincike, adana al’adu da ƙarfafa rubuce-rubucen Hausa.

Akwai wani muhimmin al’amari da ya kamata a lura da shi: adabin baka da na rubuce-rubuce na iya ɓacewa ko kuma a kasa fahimtar zurfinsa idan ba a adana su, an rubuta su, an kuma nazarce su yadda ya kamata ba.

Saboda haka, cibiyar da aka tsara ƙaddamarwa a wannan taro na iya zama wata muhimmiyar dama ta adana tarihin Hausa da ayyukan waɗanda suka bayar da gudunmawa ga bunƙasarsa.

Yadda aka gudanar da taron:

An fara taron ne a ranar Lahadi, 8 ga Nuwamba, 2026, da wani shiri na musamman na gabatar da waƙoƙi, inda Alan Waƙa ya jagoranci mawaka daban-daban a ɗakin taro na Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE) da ke Katsina. Shirin ya gudana da daddare, daga ƙarfe bakwai zuwa goma sha ɗaya, inda mawaka irin su Fati Nijar, Shalelen Zariya, Sa’idu Ja’afar Singa, Fati Khalil da Miftahu suka baje kolin basirarsu.

A nasa jawabin, Ala ya nuna godiya ga shugaban Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA), Farfesa Mohammed Khalid Othman, bisa wannan karramawa, tare da godiya ga kwamitin shirya taron da duk waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen ganin an gudanar da shi.

A rana ta biyu, an gudanar da babban zaman taron a ɗakin taro na Hillside Royal Suites da ke Katsina. Taron, wanda Sashen Nazarin Harshen Hausa na FUDMA ya shirya tare da haɗin gwiwar Cibiyar Nazarin Harshen Hausa, Tarihi, Abubuwan Tarihi da Adanawa ta Hanyar Fasahar Zamani, ya haɗa sarakuna, malamai, masana, masu bincike, marubuta da ɗalibai daga wurare daban-daban.

Daga cikin manyan baƙin da suka halarci buɗe taron akwai Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman; Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero; Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar; Sarkin Lafia, Mai Shari’a Sidi Muhammad Bage; da Sarkin Katsinan Maradi na Jamhuriyar Nijar, Alhaji Ahmed Ali Zaki.

A jawabin maraba, shugaban jami’ar, Farfesa Othman, ya bayyana muhimmancin nazarin ayyukan Ala a lokacin da marubucin yake raye, domin hakan yana ba masu bincike damar tattaunawa da shi kai tsaye, tare da samun damar jin ƙarin haske kan ayyukansa. Ya kuma jaddada muhimmancin harshen Hausa wajen isar da ilimi, al’adu da tunanin al’umma.

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda ya yi magana a madadin sarakunan da suka halarta, ya yaba da shirin, yana mai cewa nazarin ayyukan Ala zai amfani harshen Hausa da adabinsa. Ya bayyana cewa waƙoƙin mawaƙin sun haɗa nishaɗantarwa da ilmantarwa, tare da ƙarfafa tunanin al’umma.

Shi kuwa shugaban taron, Ambasada Ahmad Rufai Abubakar, ya bayyana Ala a matsayin ma’ajiya ta ilimi, musamman ganin yadda waƙoƙinsa ke adana saƙonni da abubuwan tarihi domin al’umma ta yanzu da masu zuwa. Wazirin Katsina, Alhaji Ibrahim Ida, ya kuma bayyana yadda mawaƙin ke amfani da waƙa wajen isar da damuwar al’umma kan shugabanci, ci gaba da zamantakewa.

Daga cikin muhimman abubuwan da aka tsara a lokacin taron akwai ƙaddamar da Cibiyar Nazarin Harshen Hausa, Tarihi, Abubuwan Tarihi da Adanawa ta Hanyar Fasahar Zamani. An kuma tsara bikin karrama waɗanda suka yi nasara a gasar gajerun labarai kan matsalar rashin tsaro a Arewacin Nijeriya, tare da ƙaddamar da kundin labarai 30 da aka zaɓa daga cikin rubuce-rubucen da suka shiga gasar.

A gasar, Ruƙayya Ibrahim Lawal daga Jihar Sakkwato, Nana Aicha Hamissou daga Maraɗi a Jamhuriyar Nijar, da Hauwa Shehu daga Jihar Kano ne suka zama zakaru uku. An bayyana cewa sama da labarai 500 ne suka shiga gasar, wadda aka tsara tun a shekarar 2024, kafin masana su tantance su, su zaɓi guda 30 da aka tattara a kundin musamman domin adanawa da karantawa.

Baya ga waɗannan shirye-shirye, taron ya ƙunshi gabatar da ƙasidu da tattaunawa kan fannoni daban-daban na ayyukan Ala, ciki har da waƙoƙin rubuce-rubuce da na baka da kuma ƙagaggun labarai. Wannan ya nuna cewa manufar taron ba wai karrama mawaƙin kawai ba ce, har ma da buɗe ƙofa ga zurfafa nazarin ayyukansa a fagen ilimi.

Idan aka haɗa sakamakon waɗannan shirye-shirye, za a fahimci cewa taron ya ba da wata muhimmiyar dama ta mayar da ayyukan Ala daga abin da ake sauraro kawai zuwa abin da ake nazari, adanawa da koyarwa. Amma babban ƙalubalen da ya rage shi ne tabbatar da cewa wannan yunƙuri ba zai tsaya a matsayin taron karramawa na ɗan lokaci ba.

Ya kamata a ci gaba da tattarawa da adana waƙoƙinsa da sauran ayyukansa, tare da ƙarfafa bincike kan dabarun rubutunsa, zaɓin kalmominsa da saƙonnin da yake isarwa. Haka kuma, ya dace a faɗaɗa irin wannan nazari zuwa sauran marubuta da mawaƙan Hausa, domin gudunmawar wannan zamani kada ta tsaya a cikin tunanin waɗanda suka rayu tare da ita.

Karrama mutum yana da muhimmanci, amma adana ayyukansa da tabbatar da cewa gudunmawarsa ba ta ɓace ba shi ne abin da zai taimaka wajen barin tarihi mai ɗorewa.

By ukarofi

Leave a Reply