Taron G20: Tinubu ya goyi bayan ƙaddamar da taron dangi akan yunwa da talauci

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Tinubu ya jinjina wa tsarin samar da haɗin-gwiwa tsakanin ƙasashe wajen murƙushe yunwa da talauci da Shugaba Luiz Inácio Lula da Silva na ƙasa Brazil ya bijiro da shi.

Tinubu ya bayyana hakan a matsayin abu mai muhimmanci ga ƙoƙarin yaƙi da yunwa da talauci a faɗin duniya da ake yi.

Ya bayyana hakan ne a yayin taron ƙasashen G20 karo na 19 da ke gudana a Rio de Janeiro na Brazil, ya na mai cewa hakan babban mataki ne na warware wasu daga cikin manyan matsalolin da ake fuskanta a duniya.

Ya ce, za a cimma nasarar hakan ne yayin da aka samu haɗin-kai tsakanin gwamnatoci da ƙungiyoyin ƙasa-da-ƙasa tare da samar da hanyoyin magance matsalolin da ke haifar da su acikin al’umma.

Shugaban ya kuma nuna buƙatar gaggawa ga majalisar gyare-gyaren tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya na ta tabbatar da cigaba da shiga lamuran da suka shafi kowane sassan duniya.

Har’ilayau, Tinubu ya jaddada cewa, Nijeriya a shirye ta ke ta wakilci Afirka a matakai daban-daban, ya na mai cewa za su cigaba da bada goyon baya ga al’amuran da zasu taimaka wajen magance ƙalubalen da ke fuskantar al’umma.

Bugu da ƙari, Tinubu ya yaba wa hukuncin G20 na bai wa Ƙungiyar Afirka (AU) damar zama mamba ta dindindin da kuma gayyato baƙin ƙasashe don su zama mambobi wanda ya ce hakan zai taimaka wajen inganta harkokin da ƙungiyar ta saka a gaba.

By Babaji