Tasirin motsa jiki ga lafiya(3)

Daga AISHA ASAS

Motsa jiki na rage ƙiba:

Daga farko dai me ke jawo ƙiba mai yawa a jikin ɗan Adam? Idan ka bi bayanan masana kan ƙiba a hankali za ka tarar da cewa, ƙiba mai yawa na samuwa ne sakamakon wasu ɗabi’u da jiki ba ya buƙata, na daga ababen da ake yi ko ake ci wanda ke ba wa jiki fiye da abinda yake buƙata, kamar ɓangaren matsƙi da ke haifar da yawaitar kitse a jikin ɗan Adam idan ya yi yawa, ko kuma ɓangaren abinci mai zaƙi idan ya yawaita, akwai kuma matsalar rashin motsa jiki wanda lokuta da dama shi ne limamin da ke jan ragamar mummunar qiba a jikin ɗan Adama. Domin da motsa jiki za ka iya ƙone kitsen da jiki ba ya buƙata.

Idan mun ɗauko dogon bayani kan yadda jiki ke haifar da ƙiba, za mu iya kwashe dogon lokaci muna abu ɗaya, wannan ne ya sa muka zaɓi yin bayanin a dunƙule.

Da yawa daga cikin waɗanda ke da qibar wuce wuri za ka same su da ɗabi’ar rashin son motsa jiki, da kuma cin abinci a kwanta ko ci yadda duk suke so ba tare da la’akari da yawan da zai yi wa jiki ba.

Wannan ɗabi’a ta hana abinci damar narkewa tare da karkasa shi zuwa kowanne muhalli ba qaramin taka rawa ta ke ba wurin samar da ƙiba ko tumbi.

Da yawa suna ganin cin abinci a kwanta ba komai ba, kuma a cikinsu ne aka fi samun masu qorafin ƙiba ta yi masu yawa ko ba su san me ke kawo masu ƙiba ko tumbi ba.

Idan mun fahimci wannan bayanin sosai, za mu gane rashin atisaye bayan cin abinci kawai zai iya zama silar samuwar ƙibar da ba a buƙata. Ba wai cin a kwanta ne matsalar ba, rashin motsa jikin wanda zai taimaka wa abincin ya samu narkewa kan lokaci.

Kamar yadda masana suka faɗa ƙiba na samuwa ne da taimakon wasu daga cikin iyalan hormones wanda bayanin yadda suke wannan aikin yake da tsayi.

Idan mun koma ɓangaren illar da ƙiba ta wuce wuri ke haifarwa jiki kuwa za mu fahimci motsa jiki ba wahala ba ne idan an yi la’akari da wahalar da ke tattare da curutan da ƙiba ke haifarwa.

Na sani a wannan zamani da qiba ta zama ƙawa ga mata, zai yi wuya wasu matan su yarda tana da illa, duba da cewa da kuɗinsu suke siyo ababen da za su sha don su yi ƙiba, waɗanda akasarinsu ma suna da nasu lahanin da za su iya yiwa jikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *