Ajandar sabuwar gwamnatin Nijeriya

Ranar 29 ga watan Mayu, rana ce da aka daɗe ana jira na ficewar gwamnatin Muhammadu Buhari da kuma bikin rantsar da Bola Ahmed Tinubu. Ana ta muhawarar ko gwamnatin da shugaban qasa Muhammadu Buhari ya jagoranta ta cika alƙawuran da ta ɗauka ko akasinta. Duk da ma dai gwamnatin ta yi ƙoƙarin kawo sauyi a fannonin ababen more rayuwa, kama daga gadar Neja ta Biyu zuwa aikin titin jirgin ƙasa da gina tituna.

Akwai tabbacin cewa gwamnatin Bola Tinubu za ta yi fama da tattalin arziki mara kyau, ƙasa mai rabe-raben kawuna da kuma tsarin tsaro mai sarƙaƙiya. Abin takaici ne yadda zamantakewa da tattalin arziki a Nijeriya ya zama a yau. Wani rahoto na baya-bayan nan ya bayyana cewa an kashe mutane 63,111 tun lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2015.

Bayanai da aka samu daga Hukumar Kula da Harkokin Tsaro ta Nijeriya (NST), wani shiri na majalisar kula da hulɗa da ƙasashen waje ta Afrika, ya nuna cewa ta’addanci kama daga ‘yan fashin daji, rikicin makiyaya da manoma, rikicin ƙabilanci, faɗace-faɗacen aungiyoyin asiri da sauransu su suka mamaye ƙasar.

Amma ba a takaitu ga gwamnatin Buhari kaɗai ba. Lokacin da Shugaba Buhari ya hau mulki a ranar 29 ga Mayu, 2015, adadin mutanen da aka kashe a Nijeriya, a cewar NST sun kai 34,972. Tun daga wannan lokacin, adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru zuwa 98,083 kamar yadda aka samu a ranar 16 ga Mayu, 2023.

Duk da cewa hare-haren Boko Haram ya ragu matuƙa, amma hare-haren da makiyaya ke yi ya bazu a yankin Arewa, inda aka yi la’akari da yadda ’yan ta’adda su ke kai hari a kwanakin baya. Yayin da kashe-kashe a galibin yankunan Kudu ya lafa, har yanzu yankin Kudu maso Gabas bai samu sauyi ba, tare da la’akari da yadda ’yan ƙungiyar IPOB su ke da mugun nufi.

A fannin tattalin arziki, labarin bai fi canja ba. A ƙarshen shekarar da ta gabata, ofishin kula da basussuka na Nijeriya (DMO) ya bayyana cewa gwamnati mai zuwa za ta gaji bashin Naira tiriliyan 77 idan har an samu lamuni na Naira tiriliyan 23 daga Babban Bankin Nijeriya (CBN).

Kamfanin ba da shawara na ƙasa-da-ƙasa, KPMG, ya bayyana cewa, yawan marasa aikin yi a Nijeriya ya ƙaru zuwa kashi 37.7 cikin 100 a shekarar 2022. Ya yi nuni da cewa adadin zai ƙara haurawa zuwa kashi 40.6 bisa 100, saboda ci gaba da samun matasa masu neman aikin yi a ƙasar.

A cikin wani sabon rahoto da aka fitar mai taken ‘KPMG Global Economy Outlook Report, H1 2023,’ ya ce, rashin aikin yi zai cigaba da zama babban ƙalubale saboda yadda ake samun buƙatuwar cigaba daga tattalin arzikin da ba yi da tabbas.

Alƙaluman talauci na baya-bayan sun yi muni sosai. Binciken da aka gudanar kan talauci ya nuna cewa, kashi 63 cikin 100 na mutanen da ke zaune a Nijeriya (mutane miliyan 133) talakawa ne masu ɗimbin yawa.

Yayin da kashi 65 na talakawa (mutane miliyan 86) ke zaune a Arewa, kashi 35 (kusan miliyan 47) suna zaune a Kudu. Talauci a faɗin jihohi ya sha banban sosai, inda ake fama da talauci mai ɗimbin yawa daga qasa da kashi 27 cikin 100 a Ondo zuwa kashi 91 cikin 100 a Sakkwato.

A yayin da fiye da rabin al’ummar ƙasar ke cikin talauci, ana kuma samun matsalar tsafta, kiwon lafiya da rashin abinci mai gina jiki. Talauci ya zama ruwan dare a yankunan karkara, inda kusan kashi 90 na mutanen karkara ke fama da talauci.

Ɓangaren ilimi da kiwon lafiya sun samu tsaiko, inda yajin aiki ya gurgunta su matuƙaya. Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta shiga yajin aikin sama da kwanaki 610 tun farkon tsohuwar gwamnati, wanda shi ne yajin aikin mafi daɗewa a zamanin mulkin dimokuraɗiyyar ƙasar nan. Hakazalika, yajin aikin da likitoci da sauran ma’aikatan lafiya suka yi a asibitocin Gwamnatin Tarayya a Nijeriya ya yi sanadin asarar sama da kwanaki 153 na aiki tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023. Duk da ƙarancin likitoci da ma’aikatan jinya, an yi ta samun adadin ma’aikatan jinya masu burin barin ƙasar zuwa wasu ƙasashe.

Yayin da Tinubu ya karvi sandar mulki a matsayin shugaban ƙasa da gwamnatin Nijeriya na 16 tun 1960 kuma zaɓaɓɓen shugaban qasa na 5 tun 1999, muna fatan da ya aikin da zai ciyar da Nijeriya gaba.

Abin farin ciki, a ganinmu, ya karvi mulki ne daga gwamnatin jam’iyya ɗaya; gwamnatin da ya kasance yana da dabara a cikinta, don taimaka masa, an kafa dokar tabbatar da cewa ya kafa majalisar ministocinsa cikin kwanaki 60. Tabbas, babban aiki na farko shine tabbatar da kwanciyar hankali a kan adalci, haɗa kai, cancanta da kuma gaskiya. Bayan zazzafar zaven gama gari da yaƙin neman zaɓe ya haifar, dole Tinubu ya jagoranci hanyoyin samun waraka. Wannan wani aiki ne da ya wajaba ya ɗauka cikin gaggawa. Ba zai iya barin wannan babban aiki ga wani ba. Dole ne ya tafiyar da tsarin sulhu wanda ya tavo buƙatu da buri na dukkan ’yan Nijeriya masu kishi.

Dole ne a magance ruɗani matasa a tsarin Nijeriya. Dole ne a yi wannan da sauri da ƙarfi. Dole ne sabon shugaban ya cika alƙawuran da ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓe, ya samar musu da kyakkyawar fahimtar juna. Bayan samar da ayyukan yi, ya kamata a samar hanyoyin cigaban tattalin arziki a Nijeriya, domin da hakan ne kaɗai ƙasar za ta cigaba.