Tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka a rubu’i na uku na 2024 – CBN

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka da kashi 3.46 a rubu’i na uku na shekarar 2024, daga kashi 3.19 a rubu’i na biyu na shekarar.

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ne ya bayyana hakan a cikin rahotonsa, inda ya ƙara da cewa yawanci an samu cigaban ne daga wasu ɓangarorin daban da na albarkatun man fetur. Rahoton ya ce hauhawar farashin ya ragu a lokacin.

CBN ya ce haɓakar da ake samu na da nasaba ne da ƙoƙarin inganta harkokin kasuwanci a ƙasar.

By ukarofi