’Yan sanda sun musanta rahoton Amnesty na zargin muzguna wa masu zanga-zangar matsin rayuwa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta musanta zarge-zargen da ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta Amnesty International Amnesty ta yi mata kan muzgunawa masu zanga-zangar tsadar rayuwa.

’Yan sanda sun bayyana zarge-zargen da cewa ƙarairayi ne marasa tushe da ke ƙoƙarin ɓata wa rundurar suna.

Cikin rahoton da ƙungiyar Amnesty International ta fitar ranar, 28 ga watan Nuwamba ya zargi ’yan sandan da kisan fararen hula masu zanga-zanga, tana mai cewa ’yan sanda sun kashe mutum 24 a jihohin shida da ke arewacin ƙasar.

To, sai dai ’yan sandan sun ce abin da bincikensu ya gano ya saɓa da rahoton na Amnesty International.

Yayin da yake jawabi ga taron manema labarai a Abuja ranar Lahadi, kakakin rundunar ’yan sandan, Muyiwa Adejobi ya ce tun bayan rahoton na Amnesty rundunar ’yan sandan ta kafa kwamiti domin gudanar da bincike.

Ya ƙara da cewa, kwamitin tare da haɗin gwiwa kwamishinonin ’yan sanda daga jihohin da alamarin ya shafa sun gudanar da zuzzurfan bincike kan rahoton, inda ya gano kura-kurai a zarge-zargen da Amnesty ya yi.

By ukarofi