Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araƙchi, ya bayyana cewa ƙasarsa ba ta ga wannan lokacin a matsayin mafi dacewa don shiga tattaunawa mai inganci da Amurka kan shirinta na nukiliya ba. Wannan sanarwa ta zo ne bayan da Iran ta dakatar da tattaunawa da Washington sakamakon harin da Amurka da Isra’ila suka kai kan wasu cibiyoyin nukiliya a watan Yuni.
Araƙchi ya ce, Iran ba za ta yanke hulɗa gaba ɗaya da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ba, sai dai duk wata ziyara daga masu bincike za ta nemi amincewar Majalisar Tsaron ƙasa ta Iran. Ya kara da cewa, akwai yiwuwar ganawa da Turawan Turai a nan gaba, amma “tushen tattaunawa” bai kafu ba tukuna.
Kasashen Turai sun yi barazanar sake tsunduma Iran cikin takunkumi na Majalisar ɗinkin Duniya ta hanyar tsarin “snapback” idan ba ta dawo tattaunawa ba. A halin yanzu, Amurka da Isra’ila sun yi gargaɗin cewa za su iya sake kai farmaki idan Tehran ta cigaba da samar da Uranium wanda zai iya kaiwa ga ƙera makaman nukiliya.
Iran ta dage cewa, ba ta da niyyar ƙera makaman nukiliya, amma za ta mayar da martani idan aka sake kawo barazana. Wannan batu ya sake tayar da jijiyoyin wuya a cikin tsarin diflomasiyya, inda ƙasashen duniya ke ƙoƙarin guje wa rikicin da zai iya rikitar da yankin.
