TETFund ta gindaya sharaɗin kammala tsofaffin ayyuka kafin bai wa makarantu sabbin tallafi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Asusun Tallafa wa Manyan Makarantu ta Nijeriya (TETFund) ta sanar da cewa duk wata jami’a, kwalejin fasaha ko kwalejin ilimi da ke da ayyukan da hukumar ta ɗauki nauyinsu amma ba a kammala su ba, ba za ta samu sabbin ayyukan tallafi a zagayen rabon kuɗaɗen shekarar 2027 ba, har sai ta kammala dukkan ayyukan da suka rage.

Shugaban Kwamitin Amintattu na TETFund, Aminu Bello Masari, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulɗa da jama’a na hukumar, Abdulmumin Oniyangi, ya fitar a ranar Laraba.

Masari ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin kawo ƙarshen jinkiri da yawan ayyukan da ake bari ba a kammala su ba a cibiyoyin ilimi masu cin gajiyar tallafin TETFund.

A cewarsa, Kwamitin Amintattun hukumar ya yanke hukunci na ƙarshe kan lamarin bayan lura da cewa cibiyoyi da dama sun kasa kammala ayyukan da aka amince musu da su cikin wa’adin da aka tsara.

“Mun yanke shawarar cewa duk cibiyar da ke da ayyukan da suka makara ko aka yi watsi da su ba za a amince mata da sabbin ayyuka ba a zagayen tallafin shekarar 2027,” inji Masari.

Ya bayyana cewa an umarci cibiyoyin da abin ya shafa su yi amfani da kuɗaɗen tallafin da suke samu na shekara-shekara da na shiyyoyi da kuma na manyan ayyuka wajen kammala tsofaffin ayyukansu kafin neman sababbi.

Masari ya amince cewa a baya hauhawar farashin kayan gini kamar siminti, ƙarafan gini, kayan famfo da na lantarki ya taimaka wajen jinkirta wasu ayyuka.

Saboda haka, ya ce TETFund ta ƙirƙiri wani tsarin tallafi na musamman a shekarar 2023 domin taimaka wa makarantu su kammala irin waɗannan ayyuka, kuma hakan ya haifar da gagarumin ci gaba.

Sai dai ya nuna damuwa cewa duk da wannan ƙarin tallafi, har yanzu ana ci gaba da samun sabbin ayyukan da suke makara.

A cewarsa, abin da ke haddasa hakan yanzu ba ƙarancin kuɗi ba ne, illa sauye-sauyen shugabancin cibiyoyi da kuma jinkirin biyan kuɗin ‘yan kwangila.

Ya ce wasu shugabannin makarantu kan fi karkata ga fara sabbin ayyuka maimakon kammala waɗanda suka gada, lamarin da ke haddasa asarar kuɗaɗen gwamnati.

Masari ya jaddada cewa daga yanzu ba za a ƙara lamuntar siyasa ko matsalolin gudanarwa su zama sanadin durƙusar da ayyukan da TETFund ke ɗaukar nauyi ba.

A sabon tsarin, ya ce duk cibiyoyin da abin ya shafa za su tattara jerin ayyukan da suka wuce watanni shida ba tare da an kammala su ba, su bayyana dalilan jinkirin, tare da gabatar da hanyoyin magance matsalolin.

Haka kuma za su tantance ayyukan bisa muhimmancinsu, su gabatar da ƙiyasin kuɗin da ake buƙata domin kammala su, tare da ƙarfafa tsarin sa ido ta hannun sassan tsare-tsare da kula da gine-gine na makarantun.

Domin tabbatar da bin wannan umarni, Masari ya ce tawagogin sa ido na TETFund, waɗanda suka haɗa da mambobin kwamitin amintattu da ƙwararrun jami’ai, za su kai ziyarar duba ayyukan a cibiyoyin da abin ya shafa tsakanin watan Agusta da Satumban 2026.

Rahotannin da za a tattara daga waɗannan ziyarce-ziyarcen za a tattauna su a taron kwamitin da za a gudanar a watan Oktoban 2026, inda za a yanke hukuncin cibiyoyin da za su cancanci samun sabbin ayyuka a kasafin tallafin shekarar 2027.

TETFund dai ita ce babbar hukumar gwamnatin tarayya da ke tallafa wa jami’o’in gwamnati, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi wajen samar da gine-gine, dakunan gwaje-gwaje, ɗakunan karatu, horar da malamai, bincike da sauran manyan ayyukan bunƙasa ilimi.

By ukarofi

Leave a Reply