Tikitin Muslim-Muslim ya jawo min baƙin jini a cocina – Remi Tinubu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Uwargidan Shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa zaɓin da mijinta ya yi na takarar shugaban ƙasa a 2023 ya jawo mata matsala.

Ta ce, zaɓin yin takara da Tinubu ya yi a kan tsarin tikitin Muslim-Muslim ya jefa ta cikin mara daɗi a cocinta, inda aka ware ta a gefe.

Oluremi Tinubu ta bayyana haka a cikin sabon littafinta mai shafi 52 da ta fitar don murnar cikar shekaru 65 da haihuwa.

A cikin littafin da aka yi wa taken – ‘The Journey of Grace: Giɓing Thanks in All Things’, Oluremi Tinubu ta ce cocinta ya dare.

Ta bayyana yadda cocin Redeemed Christian Church of God ya rabu gida-gida, inda wasu suka yi watsi da ita saboda wannan zaɓi na mai gidanta.

Sanata Oluremi ta bayyana cewa wannan ya nuna yadda jama’a ke da ra’ayin siyasa daban-daban duk da cewa coci guda su ke zuwa yin bauta.

Ta ce, “Na gane haka a lokacin da ya ke nema a zaɓe ni Sanata, na kai hotunan yaƙin neman zaɓena, amma jama’a su ka yi biris da su. Daga wannan lokaci ban kuma irin wannan ba.”

Uwargidan Shugaban ƙasa ta bayyana cewa duk da wannan kiyayya da ta fuskanta saboda mai gidanta, wannan bai rage mata karsashi wajen bauta a cocin ba.

“Duk da wannan kiyayya, wasu na ƙara min kwarin gwiwa, musamman dattawan. Su kan ce na dage da addu’a.”

Uwargidar ƙasa ta ce, ba ta bar aikin cocin da ta yi tsawon shekaru 15 ba, inda ta tashi daga mai aiki zuwa Mataimakiyar Fasto a shekarar 2018.

Ta ce, yawan zuwa coci da yin ibada na daga cikin abubuwan da su ka taimaka mata wajen samun nasara da kau da kai dga maganganun masu adawa da zaɓin Tinubu.

A cikin littafinta, ta bayyana yadda take yin yafiya ga duk waɗanda su ka ci amanar mijinta a lokacin yaƙin zaɓe na 2023.

By ukarofi