Tinubu da Shettima sun karɓi baƙoncin tawagar matasa a taron ilimintarwa

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

A wani yunƙuri na inganta matasa a Nijeriya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Mataimakinsa Kashim Shettima da Shugaban Jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje sun shirya jagorantar taron ilimintarwa na matasa a ranakun 3 zuwa 5 ga watan Satumban 2024 a Fadar shugaban ƙasa.

An shirya taron ne ta ofishin shugaban matasan jam’iyyar APC na Ƙasa domin ƙarfafa alaƙa tsakanin gwamnati da matasan da kuma shiga cikin harkar tsare-tsaren shugaba Bola Ahmed Tinubu na samar da cigaba mai ɗorewa a Nijeriya.

Cikin ababen da taron ya ƙunsa akwai fage na tattaunawa tsakanin gwamnati da matasan inda za a fayyace batutuwa da dama kamar su; ilimi, fasaha, bunƙasa tattalin arziƙi, inganta makarantu da makamantan su.

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima zai buɗe taron kwana uku yayin da shugaba Tinubu zai gabatar da jawabi tare da karɓar jadawalin tsare-tsaren taron.

Dakta Dayo Israel wanda shi ne shugaban matasan na APC, ya ce taron mataki ne na tabbatar da ba iya jin muryar matasa a ƙasa ba, har ma zai taka rawar gani wajen samar da cigaba a Nijeriya, ya na mai bada misali da irin hoɓɓasa da shugaban ƙasa da Mataimakinsa suka yi na damawa da su a harkokin gwamnati.

Kazalika, ƙofa a buɗe ta ke wajen halartar taron bayan ga yin rijista wanda ake sa ran za a karɓi aƙalla mutane 3,000 wanda hakan zai zama ɗaya daga cikin manyan zauren tattaunawa da matasa a zamanin nan.

By Babaji