Tinubu na ƙoƙarin maida Nijeriya mai jam’iyya ɗaya – ADC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar ADC ta ce sauya sheƙar da wasu gwamnonin jihohi suka yi zuwa jam’iyya mai mulki ya nuna yadda Shugaba Bola Tinubu, ke ƙoƙarin mayar da Nijeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya.

A wata sanarwa da Bolaji Abdullahi, mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, ya fitar, ya ce jam’iyyun adawa ba su damu da abin da ya kira “cin amanar siyasa” da gwamnonin suka yi ba.

Ya ce zaɓen 2027 ba zai zama takara tsakanin jam’iyyu kawai ba, sai dai ya zama gwagwarmaya tsakanin talakawan Nijeriya da gwamnatin da ta jefa rayuwar talakawa cikin wahala.

Abdullahi, ya bayyana cewa komawar gwamnonin jihohin Enugu da Bayelsa zuwa jam’iyyar APC, ta tabbatar da cewa Shugaba Tinubu, na da niyyar raunana dimokuraɗiyya da jam’iyyun adawa a ƙasar nan.

Ya ƙara da cewa duk da cewar gwamnonin sun koma jam’iyya mai mulki a zahirin gaskiya sun bar jama’arsu ne tare da komawa jam’iyyar da ta gaza ciyar da ƙasa gaba.

A cewar Abdullahi, ’yan Nijeriya da dama suna cikin wahala saboda gazawar gwamnatin APC, hauhawar farashin kayan abinci, rashin ayyukan yi, matsalar tsaro, rashin ingantaccen tsarin kiwon lafiya, da cin hanci da rashawa.

Ya ce ’yan Nijeriya sun yi tsammanin gwamnonin adawa za su yi tsayin daka su kare jama’a da kawo mafita, amma maimakon haka, wasu daga cikinsu sun shiga jam’iyyar mai mulki saboda son rai.

Abdullahi, ya kuma ce duk da APC na murna da samun waɗancan gwamnoni, ADC da sauran jam’iyyun adawa suna farin ciki saboda yanzu ’yan Nijeriya za su iya gane waɗanda za su tsaya domin ceto ƙasar nan.

Ya ƙarƙare da cewa zaɓen 2027 zai zama takara kai-tsaye tsakanin talakawan Nijeriya da gwamnatin Shugaba Tinubu ta Jam’iyyar APC.

By ukarofi