
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya tawagar Flamingos, wato ‘yan wasan Nijeriya mata ‘yan ƙasa da shekara 17 bisa doke Brazil da ci 3 da 1 wasan gab da na ƙarshe na gasar Kofin Duniya na 2026 da ake gudanarwa a Moroko. Kociyan ‘yan wasan, Hakeem Busari ya bayyana cewa, rashin bai wa ‘yan ƙasar kudancin Amurkan dama gagarumar nasara ce ga Flamingos.
Wannan nasara ta sa Nijeriya ta kai matakin wasan ƙarshe a karon farko a tarihinta a gasar, inda a yanzu tawagar za ra kara da Japan a wasan ƙarshe a ranar Asabar, 7 ga Nuwamba, 2026, Busari ya bayyana ƙwarin-gwiwarsu ta samun nasara a wasan. A cewar sashen wasannin PUNCH, ‘yan Flamingos ɗin baya ga nasarar da suka samu a wasan, sun kuma hana Brazil kataɓus, inda suka kai mata jimillar farmaki 35, yayin da ita Brazil ke sa bakwai.
A sanarwar da Kakakin Shugaban Ƙasa Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana wannan nasara a matsayin abin alfahari da ya jefa miliyoyin ‘yan Nijeriya cikin farin ciki a gida da wajen ƙasar.
Ya yaba wa tawagar masu horar da ‘yan wasan da gudumawar da suka bayar wajen kai ga samun nasarar ‘yan wasan, yana mai kira ga Flamingos da su kasance masu mayar da hankali da ƙwarin-gwiwar samun nasara a wasan ƙarshen, inda ya kuma ba su tabbacin samun goyon bayan ‘yan Nijeriya mara iyaka.
