Tinubu ya nemi a samar da mafita ta difulomasiyya ga yaƙin Isra’ila da Palestine, inji Ministan Labarai

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nemi a samar da hanyoyin difulomasiyya domin kawo ƙarshen yaƙin Isra’ila da Palestine a taron haɗaka na ƙasashen Larabawa, a Riyadh da ke ƙasar Saudiyya.

Ministan Labarai da Wayar da kan al’umma, Mohammed Idris ya bayyana hakan wa manema labarai na Fadar shugaban ƙasa, a Riyadh.

Ya ce, Shugaba Tinubu na neman a samu hanya ta lumana da bin tsarin difulomasiyya wajen dakatar da yaƙin da ke faruwa tsakanin ƙasashen biyu.

Ministan, ya ce Nijeriya ta shiga sahun ƙasashen duniya da ke ƙoƙarin ganin an kawo ƙarshen yaƙin, ya na mai cewa matuƙar ba a bi hanyoyin ba, to akwai yiwuwar yaƙin ya haɗiɗiye yankin wanda kuma ka iya shafar duniya baki ɗaya.

Game da zuwan Shugaba Tinubu taron, Ministan ya ce kasancewar Nijeriya ƙasa ce mai muhimmanci a Afirka da ma duniya baki ɗaya, hakan ya sanya aka gayyace shi.

Ya kuma ce Nijeriya na da kusanci da yankin Gabas ta Tsakiya da ƙarfin alaƙa a tsakanin ta da ƙasashen Nahiyar Asia.

Har’ilayau, Minista Idris ya bayyana cewa, Shugaba Tinubu, a matsayinsa na mai zurfin tunani da tausayi, ya sa ya ke ganin wajibi ne ƙasashen biyu su tattauna don a samu mafita ga yaƙin da aka ɗauki sama da shekara guda ana yi.

A ranar Lahadi ne Shugaba Tinubu ya bar Abuja don halartar taron wanda musamman an shirya shi ne kan yaƙe-yaƙen Gabas ta Tsakiya.