Tinubu ya samu ƙuri’u miliyan 11 a zaɓen fidda gwanin APC na 2026 – Rahoto

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya lashe tikitin tsaya wa takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC gabanin zaɓen 2027, bayan ya samu kusan ƙuri’u miliyan 11 a zaɓen fidda gwani da aka gudanar a faɗin ƙasar.

Sakamakon da aka tattara daga dukkan jihohi 36 da babban birnin tarayya ya nuna Tinubu ya samu gagarumin rinjaye a kan abokin takararsa Stanley Osifo, lamarin da ya ƙara tabbatar da ƙarfin tasirinsa a cikin jam’iyyar mai mulki.

Sakamakon da aka sanar a taron tattara ƙuri’u da ke gudana a Abuja ya nuna cewa a jimlace, Tinubu ya samu ƙuri’u 10,990,000 yayin da abokin takararsa ya samu 16,504 a zaɓen da aka gudanar a mazabu 8,809 a faɗin Najeriya.

Jaddawalin Sakamakon Zaɓen Fidda Gwanin Shugaban Kasa Bola Tinubu, Inda Ya Samu Kuri’u Kusan Miliyan Sha Ɗaya A Jihohi 36 Har Da Abuja

Ga jaddawalin sakamakon jihohin kamar yadda rahotanni suka bayyana:

  1. Lagos: 814,988
  2. Adamawa: 644,149
  3. Kaduna: 618,914
  4. Imo: 582,960
  5. Kano: 500,852
  6. Katsina: 467,003
  7. Gombe: 450,517
  8. Borno: 414,988
  9. Delta: 407,646
  10. Akwa Ibom: 389,197
  11. Enugu: 383,382
  12. Benue: 374,787
  13. Plateau: 241,720
  14. Bayelsa: 227,192
  15. Ebonyi: 207,579
  16. Jigawa: 206,520
  17. Kogi: 197,370
  18. Taraba: 183,698
  19. Ondo: 181,996
  20. Niger: 175,487
  21. Abia: 161,005
  22. Bauchi: 156,541
  23. Ogun: 322,485
  24. Zamfara: 321,579
  25. Kwara: 310,990
  26. Sokoto: 301,000
  27. Kebbi: 292,972
  28. Nasarawa: 285,436
  29. Rivers: 280,082
  30. Yobe: 253,804
  31. Cross River: 113,911
  32. Edo: 121,098
  33. Oyo: 142,754
  34. Osun: 100,888
  35. Ekiti: 85,340
  36. Anambra: 43,034
  37. FCT: 36,103
  38. Jimilla: 10.99m
By Babaji