Atiku, Amaechi da Hayatu-Deen za su fafata a zaɓen fidda gwanin takarar shugaban ƙasa na ADC a yau

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, tsohon gwamnan Ribas Rotimi Amaechi da kuma masanin tattali, Mohammed Hayatu-Deen, sun shirya karawa a zaɓen fidda gwanin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar adawa ta ADC a yau Litinin.

Za a gudanar da zaɓen ne a ƙarƙashin jagorancin Shugaban jam’iyyar na Ƙasa, David Mark yayin tunkarar babban zaɓen 2027.

Rahotanni sun bayyana cewa, waɗannan ukun sune ‘yan gaba-gaba da ke neman tikitin shigar takarar shugaban ƙasar da za a yi a 2027, inda majiyoyi suka ce zaɓen zai zama fafatawa mai zafi a ɓangaren adawar.

Hakan na zuwa ne bayan da kwamitin jam’iyyar, ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Kuros Riba, Liyel Imoke, ya kammala aikin tantance masu neman shiga takarar.

Da fari, jagorancin jam’iyyar ƙarƙashin David Mark ya yi ƙoƙarin a tsayar da ɗan takara ɗaya ta hanyar yin sulhu a tsakanin masu nema, amma hakan bai yi nasara ba. Don haka ne ADC ta amince da a gudanar da zaɓen fidda gwanin.

Haka kuma, akan haka ne jam’iyyar ta kafa kwamitin zaɓen shugaban ƙasa ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, da Farfesa Yisa Gana a matsayin sakatare domin sun jagoranci al’amarin.

Sauran mambobin sun haɗa da Manjo’Janar. Adamu Jalingo, Dakta Auwalu Anwar, Cif Emenike Ikechi, Dakta Macaulay Iyare, Tajudeen Bakare, Elder Ubolo Itodo Okpanachi, Zainab Buba Galadima, Uzoamaka Onyeama, da kuma Manjo-Janar Muhammad Inuwa Idris.

A cewar Sakataren jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, an tura jami’an zaɓe a dukkan sassan Nijeriya domin gudanar da zaɓen, yana mai cewa za a tabbatar da gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci.

By Babaji