Ku yi amfani da titin Kachia zuwa Bwari yayin cinkoson na Abuja zuwa Kaduna – FRSC ga masu ababen hawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa FRSC, ta shawarci masu ababen hawa da ke amfani da babban titin Abuja zuwa Kaduna sakamakon cinkoso da ak samu a kwanan nan saboda masu zirga-zirgar tafiye-tafiyen bikin Sallah.

Haka kuma, ta bayyana cigaba da aikin gina titin da ruwan sama mai ƙarfi a matsayin ababen da ke haifar ƙalubalen cinkoso.

A wata sanarwa da Kwamandan Sashe na Kaduna, Andrew Longkam ya fitar, ya ce yankin Nasarawa Azara tsakanin garuruwan Katari da Jere ne aka fi samun cinkoson, lamarin da ke haddasa jinkiri da wahalhalun tafiye-tafiye.

Hukumar ta ƙara da cewa, rashin kiyaye dokokin titi kamar bin hannun da ya dace na cikin abin da ya ta’azzara cinkoson.

Akan haka ne hukumar ta shawarci masu ababen hawa da ke tafiya daga Kaduna zuwa Abuja da su amfani da hanyar ta bi ta Kachia, Maraban Kubacha, Jere, Bwari da Dutse a Abuja.

Haka ma masu tafiya daga Abuja zuwa Kaduna da su bi hanyar, tana mai gargaɗin su da su ƙaurace wa tuƙin ganganci da kiyaye dokokin tuƙi.

By Babaji