2027: ADC ta tabbatar da Malami da wasu a matsayin ‘yan takarar Kebbi

Spread the love

Jam’iyyar ADC ta tabbatar da tsohon Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Ƙasa, Abubakar Malami, a matsayin ɗan takararta na gwamna a jihar Kebbi domin zaɓen 2027.

A sanarwar da mai taimaka masa kan yaɗa labarai, Mohammed Doka, ya fitar, jam’iyyar ta kuma tabbatar da Aminu Bande, Ibrahim Mera da Garba Limi a matsayin ‘yan takarar Sanata na Kebbi ta Tsakiya, Arewa da Kudu.

Jam’iyyar ta yaba wa shugabanni da magoya baya bisa goyon bayan da suke bai wa ADC, tana mai cewa za ta ci gaba da jajircewa wajen samar da shugabanci nagari, tsaro da ci gaba mai ɗorewa.

A jihar Kwara kuwa, tsohon ɗan majalisar wakilai, Zakari Mohammed, ya lashe tikitin gwamna na ADC bayan an zaɓe shi a matsayin ɗan takarar maslaha, inda ya samu ƙuri’u 18,860.

Haka kuma, Risikat Abdullahi, Iyiola Oyedepo da Mallam Taoheed Usman sun samu tikitin Sanata na Kwara ta Tsakiya, Kudu da Arewa. INEC ta sanya ido kan gudanar da zaɓen fidda gwanin jam’iyyar a jihar.

By Babaji