“Ba a haifar jarumar mace, ginata ake yi”
Daga AISHA ASAS
A cikin wannan shafi mai farin jini na Gimbiya, muna ci gaba da haskaka rayuwar mata jarumai, waɗanda suka tsallake rijiya da baya, suka fuskanci ƙalubalai masu tsanani, amma suka tsaya tsayin daka har suka zama abin koyi ga al’umma.
Kamar yadda ku ka sani, wannan shafi ba kawai shafin bayar da labaran rayuwar mata ba ne, wuri ne na ilmantarwa da tunatarwa, inda ake fito da rayuwar mata domin ta zama madubi ga sauran mata masu neman hanya.
A wannan mako, hasken shafin ya karkata ne zuwa ga rayuwar Marie Curie, macen da rayuwarta ta kasance cike da gwagwarmaya tun daga tushe, amma ta ƙare da sauya akalar duniya. Ba wai kawai ta yi nasara a rayuwa ba, ta kuma taka rawa wajen sauya yadda bil’adama ke fahimtar asalin halitta da kimiyya.
Shafin Gimbiya zai zurfafa cikin rayuwarta daga farkon ƙalubale zuwa ƙololuwar nasarar da ta samu, domin fito da darussa masu ƙarfi ga kowace mace da ke kokarin tsayawa da ƙafafunta a duniya mai cike da ƙalubale. Idan kun shirya Aisha Asas ce ɗauke da tarihin jarumar mace kuma sarauniyar kimiyya, Marie Curie.
Shin wacce ce Marie Curie?
An haifi Marie Curie da sunan yanka na Maria Skłodowska a shekarar 1867, a lokacin da ake tsananin danniya da takurawa ga ilimi da ‘yancin tunani, wato dai akwai katangar ƙarfe tsakanin mutum da irin tunanin ci gaba da zai iya yi, kenan ba a ba wa kimiya ‘yancin bajikoli ba. Amma duk da wannan yanayi mai nauyi, ta taso da zuciyar da ba ta yarda a takaita ta ba.
Ta fito daga cikin iyali masu kishin ilimi amma marasa yalwar arziki. Mahaifinta malami ne da ke koyar da kimiyya, yayin da mahaifiyarta ke jagorantar makaranta. Duk da haka, wannan matsayin bai kare su daga tsangwama ba.
Mulkin Rasha ya takaita ‘yancin ilimi, musamman ga ‘yan Poland. Mahaifinta ya rasa aikinsa saboda rashin bin dokokin gwamnati, yayin da mahaifiyarta ta rasu sakamakon cutar tarin fuka wato tarin TB, a lokacin da Marie ke da shekaru 11.
Wannan rashi ya girgiza rayuwarta, saidai bai sare mata gwiwa ba. A maimakon haka, ya ƙara mata fahimtar cewa rayuwa na buƙatar juriya da tsayuwa.
Yaushe Marie ta fara kwaɗayin ilimi?
Tun tana ƙarama, Marie ta nuna hazaƙa da kaifin tunani na musamman. Saidai kasancewarta mace ya hana ta shiga jami’a a ƙasarta, sakamakon danniyar ‘yancin ilimin mata da ke akwai.
Duk da haka ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, ta nemi hanya mafi sauƙi da hannunta zai iya kai ga ilimin, don haka idonta bai hango komai ba face shiga jami’ar da ake kira ‘Flying University’, wata cibiyar ilimi ta ɓoye da ke koyar da kimiyya da ilimi a sirrance. Wannan mataki ya nuna irin juriyar da take da ita wajen neman ilimi duk da tsananin hatsarin da ke ciki
A nan ne ta fahimci tare da faɗar cewa: ilimi ba kawai hanya ce ta samun aiki ba, hanya ce ta samun ‘yanci.
Akan ce ana gane nagartar mutum ta hanyar irin sadaukarwar da ya yi ga makusantanshi. Shin wacce irin sadaukarwa ce Marie ta fara yi ga makusantan ta?
Domin tallafa wa iyalinta, Marie ta yi aiki a matsayin governess na tsawon shekaru. Ba don komai ta yi hakan ba kuwa face don ta tura kuɗin da take samu ga ‘yar uwarta domin ta yi karatu.Ta jinkirta nata burin, amma ba ta manta da shi ba. Bayan komai ya daidai ta ne ta ci gaba da karatu da kanta, amma fa sai da ta yi ƙaura zuwa ƙasar Faransa.
Ya rayuwar Marie Curie ta kasance a Faransa. Ko an fuskanci ƙalubalai?
Lokacin da Marie Curie ta isa Paris a farkon shekarun 1890, ba ta zo da komai ba face burinta da kuma zuciyar da ta saba da wahala. Rayuwa ba ta tarɓe ta da jin daɗi ko sauƙi ba, maimakon haka rayuwa ta buɗe mata ƙofa ne da yunwa, kaɗaici da kuma matsanancin sanyi
A cikin wani ƙaramin ɗaki mai sanyi da ba shi da dumama, ta fara sabuwar rayuwarta. Lokutan hunturu su kan zama kamar azaba, iska mai ƙaifi na shiga bangon ɗakin, yana haddasa sanyi mai tsanani da ke shiga har cikin ƙasusuwa. Ba ta da isasshen tufafi, balle abinci mai kyau.
A wasu ranaku, yunwa kan yi mata yawa har ta kasa tsayawa da ƙafafunta. Sau da dama tana suma a cikin ɗakin karatunta. Amma duk da wannan hali, akwai abu ɗaya da ba ya gushewa a zuciyarta, wato ƙudurinta na yin nasara.
A cikin ɗakunan karatu na Sorbonne, ana ganin ta a matsayin wata ɗaliba mai nutsuwa, mai yawan tunani, wadda ba ta damu da wahalhalun rayuwa ba. Amma a bayan wannan nutsuwa akwai labari mai cike da azaba, wato labarin mace da ke fafutukar rayuwa da ilimi a lokaci guda.
Ba ta neman suna ko ɗaukaka, abin da take nema shi ne kada a bar ta a baya. Kada a rufe mata kofar ilimi kamar yadda aka taɓa yi a ƙasarta.
A hankali, wahala ta fara juya zuwa ƙarfi. Yunwa ta zama darasi. Sanyi ya zama ɗumi. Kuma wannan gwajin da rayuwa ta yi mata ne ya gina mace mai ƙarfi, wadda daga baya za ta girgiza duniya.
Bari nu koma ɓangaren zamantakewa. Ko Marie ta taɓa aure?
A cikin wannan tafiya ta wahala, rayuwa ta kawo mata haɗuwa da Pierre Curie, mutum mai nutsuwa, mai zurfin tunani, kuma mai irin wannan kishin kimiyya da take da.
Abin da ya haɗa su bai tsaya ga soyayya ba. Wata irin fahimta ce mai zurfi, wato fahimtar cewa su biyun suna kallon duniya ne da ido iri ɗaya: ido na bincike, na tambaya, da na neman gaskiya.
Aurensu bai zama mafaka daga wahala ba, saidai ya zama haɗin gwiwar da ya haifar da juyin juya hali a kimiyya.
A cikin wani ƙaramin ɗakin gwaje-gwaje mai cike da ƙura da danshi, suka fara binciken da duniya ba ta taɓa gani ba. Ba su da kayan aiki na zamani, ba su da isasshen tallafi, amma suna da abu mafi muhimmanci, wato imani da abin da suke nema.
An ce bayan wuya sai daɗi. Wacce nasara ce Marie Curie ta fara samu?
Ba za mu iya amsa wa Marie wannan karin magana ba, domin a tata rayuwa kusan ƙalubalai da nasarorin ta a tare suke tafiya. Inda takan samu nasara a yau, gobe ta samu kanta a wani ƙalubalen kafin wata nasarar ta yi sallama.
Saidai za mu iya cewa yana daga cikin nasarar ta ta farko, yayin da take nazarin uranium, Marie Curie ta fara lura da wani abu da ya saɓa wa duk abin da aka sani a lokacin. Radiation da take gani ba ya sauyawa, ko da an canza yanayin sinadarin. Wannan abu ya tada mata hankali.
A hankali, ta fara fahimtar cewa, wannan ƙarfin ba daga waje yake fitowa ba, yana fitowa ne daga cikin atom kansa.
A wancan lokaci, masana kimiyya sun yi imanin cewa, atom ba ya rabuwa. Amma abin da ta gano ya rusa wannan fahimta gaba ɗaya.
Bayan watanni na aiki mai tsanani, ta hanyar murƙushe duwatsu, tace sinadarai, da aiki tuƙuru kuma mai wahala, ta gano sabbin abubuwa guda biyu: polonium da radium.
Wannan kuwa ba kawai gano sinadarai ba ne, gano wani sabon babi ne a tarihin bil’adama.
Abin da ta gano ya buɗe ƙofa ga sabbin fannoni kamar Radiology, wanda a yau ke taimaka wa wajen gano cututtuka da ceton rayuka.
Ko wannan binciken da ta yi ya tsaya a matsayin cigaba kawai, ko kuwa ya haifar da wani sakamakon?
Yayin da duniya ke alfahari da godiya ga wannan bincike da ya samar da hanyar ceton rai, hakan ba zai hanata ganin babban hatsarin da wannan bincike ya haifar ba. Binciken ya samar da hanyar ceton rai, kuma a lokaci guda ya zama tushen wasu makamai masu hadari. Waɗanda a halin yanzu muke kuka da su ko kuma in ce suka yi sanadiyyar rasa rayuka marar misaltuwa.
Don haka bayyana matsayar wannan bincike abu ne mai rikitarwa saidai kawai mu ɗora shi kan batun nan da ya ce: ilimi na iya zama haske, amma kuma a wani hannu yana iya zama wuta.
Wane irin taimako Marie Curie ta bayar a lokutan yaƙi?
Lokacin da Yaƙin Duniya na ɗaya (World War I) ya ɓarke, mutane da dama sun tsere don gujewa haɗari. Saidai a ɓangaren Marie Curie sam ba haka ba ne.
Ta ga wata matsala mai girma: sojoji na mutuwa ba saboda raunuka kawai ba, sai saboda rashin sanin inda raunukan suke. Don haka ta yanke shawarar ɗaukar mataki, ma’am amfani da iliminta don kawo ɗauki a wannan ɓangaren.
Ta ƙirƙiri motocin X-ray masu motsi, waɗanda daga baya aka kira “Little Curies.” Ba ta tsaya kan tsarawa ba, ta koyar da yadda ake amfani da su, ta horar da mata, har ma ta shiga filin yaƙi da kanta.
A cikin hayaniyar harbe-harbe da tashin hankali, ana iya ganin ta tana aiki cikin nutsuwa, tana taimaka wa likitoci gano harsasai a jikin sojoji.
A sakamakon wannan aiki, an ceci rayukan dubban mutane. Kimiyya ta sauka daga littafi zuwa aikace.
Saidai wannan nasara ta zo da farashi mai girma wanda ta biya da lafiyar ta. Shin wane irin farashi ne Marie Curie ta biya na wannan namijin aiki da ta yi?
Ku tari amsar wannan tambayar a mako na gaba.
