Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya ƙaddamar da zagaye na biyu na rabon tallafin inganta makarantu (School Improvement Grants) na kimanin Naira ₦6,116,343,477.00, wanda zai amfani makarantu 110 a faɗin jihar Katsina.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin bikin ƙaddamar da tallafin da aka gudanar a ofishin aikin TESS da ke Katsina, inda ya bayyana shirin a matsayin hujja ƙarara ta yadda gwamnatinsa ke bai wa ɓangaren ilimi muhimmanci domin inganta darajar ilimi.
Gwamna Raɗɗa ya jaddada cewa ilimi na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba, domin babu yadda za a samu ci gaba mai ɗorewa face ta hanyar saka hannun jari a rayuwar al’umma. Ya bayyana ƙudurinsa na gina tsarin ilimi mai inganci, adalci, da rikon amana wanda zai bai wa yara damar gogayya da takwarorinsu a duniya ta zamani.
“Manufarmu ita ce gina tsarin ilimi mai adalci, mai amfani, mai gaskiya, wanda zai shirya yaranmu yadda za su iya gogayya a wannan zamani,” in ji gwamnan.
Shirin tallafin inganta makarantu wata muhimmiyar hanya ce ta ƙarfafa makarantu a matakin ƙasa, ta hanyar ba su tallafi kai tsaye domin magance matsalolin gine-gine da kayan koyarwa.
Zagaye na biyu na tallafin zai haɗa da gina ƙarin ɗakunan karatu, gyaran gine-ginen makarantu da suka lalace, samar da banɗakuna masu kula da bambancin jinsi, da kuma samar da tsaftataccen ruwan sha bisa ƙa’idojin mafi ƙaranci na UBEC.
Hakazalika, Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da sabon babban ɗakin taro mai ɗaukar mutane 500 a ofishin aikin TESS, sannan ya raba kayan koyarwa na musamman ga yara masu buƙata ta musamman a makarantar makafi ta Katsina da kuma makarantar kurame ta Malumfashi.
Gwamnan ya bayyana cewa aikin TESS ya samu nasarori masu yawa wajen bunƙasa ɓangaren ilimi. Ta hanyar aikin, an raba littattafan lissafi, Turanci da Computer Studies ga ɗalibai.
Haka kuma an samar wa malamai da na’urorin tablet, yayin da malamai 28,000 suka samu horo kan dabarun koyarwa na zamani, gudanar da aji, da tsarin koyarwa mai tsari.
“Domin tallafawa ilimi mai bai wa kowa dama, an samar da kayan koyarwa da na’urorin taimako ga makarantu masu kula da yara masu buƙata ta musamman. Bugu da ƙari, an girke kyamarorin CCTV a makarantu 130 domin ƙara tsaro da samar da muhalli mai aminci ga ɗalibai. Haka kuma an bai wa jami’an sa ido da tantancewa na dukkanin hukumomin ilimi na ƙananan hukumomi 34 babura domin sauƙaƙa aikin sa ido a yankunan karkara,” in ji gwamnan.
Gwamna Raɗɗa ya yi kira ga kwamitocin kula da makarantu, iyaye, shugabannin al’umma da malamai da su mara wa wannan ƙoƙari baya tare da tabbatar da amfani da ayyukan yadda ya kamata da kuma kula da su.
“Dole ne a yi amfani da waɗannan kuɗaɗe cikin gaskiya, tsantseni da riƙon amana, bisa ga ƙa’idojin da aka amince da su,” gwamnan ya jaddada.
Gwamnatin jihar ta kafa kwamitin sa ido na musamman wanda ya ƙunshi wakilan hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa, tawagar sa ido da tantance ayyuka ta jihar, hukumar gudanar da cigaban Jihar Katsina, da kuma Ofishin Shugaban Ma’aikata na jihar. Mai kula da aikin TESS ne zai kasance sakataren kwamitin.
A cewar gwamnan, “Kwamitin sa ido zai tabbatar da cewa dukkan ayyukan sun cika ƙa’idojin mafi ƙaranci na UBEC tare da taimakawa jihar Katsina wajen samun tallafin sakamako daga Bankin Duniya da sauran hukumomin bayar da tallafi.
