Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani da uwar jam’iyar PDP ta ƙasa ta turo jihar Katsina Barista Muhammad Nura Sani ya sanar da haka a filin taro na sakatariyar jam’iyar PDP na Katsina.
Ya ce a matsayin sa shugaban kwamitin zaɓe bayan cika ƙa’idojin da hukumar zaɓe ta tanada da ƙa’idojin da jam’iyar ta tanada yana mai sanar da cewa wakilai 77,085 akayiwa rajista da ciki mutane 77,013 suka kada ƙuri’a na fidda ɗan takara.
Lado Danmarke ya lashe zaɓen fidda gwani da kuri’a 77,013 wanda yasa shugaban kwamitin ya ayyana Yakubu Lado Danmarke a matsayin ɗan takara tilo na jam’iyar PDP a jihar Katsina.
Da yake jawabi bayan ayyanashi a matsayin ɗan takarar jam’iyar PDP, Sanata Lado Danmarke yayi godiya ga ya’yan jam’iyar PDP da suka nuna masa ƙauna da karamci.
Ya ce yanzu ba lokacin maganan siyasa bane” Amma da zaran an ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe a lakacin zamu bayyana manufofin mu na siyasa.
Sanata Lado Danmarke wanda ke tsayawa takarar kujerar gwamnan Katsina a karo na uku,ya ce ya amince ya sake tsayawa takarar kujerar gwamnan Katsina.
Ya Kuma nuna godiyar sa ga zaɓaɓɓun yan takara da sauran masu ruwa da tsaki karamci da aka nuna masa.
